Aisha Abubakar
Aisha Abubakar ƴar siyasar Najeriya ce. Bayan zaɓukan shekarar 2015 da aka yi a Najeriya, an naɗa ta a matsayin Ƙaramar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Shugaba Muhammadu Buhari a karshen 2015.[1]
Aisha Abubakar | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
30 Satumba 2018 - 28 Mayu 2019 ← Aisha Alhassan - Pauline Tallen →
11 Nuwamba, 2015 - 30 Satumba 2018 - Mariam Yalwaji Katagum →
2014 - | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | jihar Sokoto, 20 ga Yuli, 1966 (58 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Mazauni | Najeriya | ||||||
Ƴan uwa | |||||||
Mahaifi | Abubakar Alhaji | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
University of Warwick (en) University of Leeds (en) | ||||||
Matakin karatu |
Bachelor of Arts (en) master's degree (en) | ||||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Wurin aiki | Abidjan, Lagos, da Abuja | ||||||
Employers | Najeriya |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Hajiya Aisha Abubakar a ranar 20 ga watan Yulin shekarar 1966 a garin Dogondaji, jihar Sakkwato. Ɗiyar tsohon ministan kudi ce. Ta yi karatun sakandare a Kwalejin Queens, Legas tsakanin 1978-84. Ta samu digirin ta na farko ne daga Jami'ar Warwick, inda ta samu digiri na farko a fannin siyasa da karatun ƙasa da ƙasa tsakanin shekarar 1987 zuwa 90. Ta kuma sami digiri na biyu a karatun ci gaba daga Jami'ar Leeds. An kuma nada ta ta kula da harkokin mata kamar yadda Misis Aisha Alhassan ta yi murabus kuma za ta ci gaba da rike matsayinta na ƙaramar ministar masana'antu, kasuwanci da saka jari.
Harkar siyasa
gyara sasheAn naɗa Aisha Abubakar ƙaramar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba jari a watan Nuwamba na shekarar 2015. Kafin wannan, ta yi aiki a Bankin Raya Ƙasashen Afirka tsakanin 1993-99.
A watan Oktoba na shekarar 2017, ta kula da ɗaukar haya daga Bankin Masana'antu (BOI), Bankin shigo da kaya daga Najeriyar da wasu ma'aikatun gwamnati. Yayin sanya hannu kan yarjejeniyar, ta bayyana cewa, manufar hukumar ita ce ta rage kudaden da ake ba kananan da matsakaitan masana'antu a ƙasar. A shekarar 2017, ta nuna cewa saboda sake sha'awar gwamnati a bangaren noma, noman koko a Najeriya zai karu da kashi 50% a 2021. Abubakar ta kuma yi kira ga hadin kan Najeriya ta hanyar rarraba kawuna a sassa daban-daban na kasar, tana mai bayanin cewa ya kamata cibiyoyin ilimi su gina mutanen da za su taimaka wajan faɗaɗa wannan. Don tunawa da ranar mata ta duniya, Abubakar ta faɗakar da mata 200 a cikin mahaifarta ta hanyar albarkatu da dabaru kan sabbin hanyoyin amfani da amfanin gona.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Minister of State for Industry, Trade and Investment, Hajiya Aisha Abubakar paid Sallah homage to Acting President Yemi Osinbajo". Blueprint Nigeria. Retrieved 2017-10-13.