Adamu Bello
Adamu Bello (an haife shi a ranar 20 ga watan Mayu, shekara ta alif ɗari tara da hamsin da daya 1951A.c) dan siyasan Najeriya ne wanda ya kasance ministan noma da raya Karkara na gwamnatin tarayya daga shekarar 2001, zuwa 2007. Ya kuma jagoranci hadaddiyar ma'aikatar noma da albarkatun ruwa a shekara ta 2007.
Adamu Bello | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
ga Janairu, 2007 - Mayu 2007 - Abba Sayyadi Ruma →
2003 - 2007 ← Sani Daura
2003 - 2007 - Abba Sayyadi Ruma → | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | 20 Mayu 1951 (73 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | Makarantar Kasuwanci ta Harvard. | ||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | civil servant (en) |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
ALHAJI ADAMU BELLO.JPG Adamu Bello | |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Bello a shekarar 1951, a garin Numan dake jihar Adamawa a Arewacin Najeriya, da ne ga mai shari'a Mohammed Bello. Ya kasance dan gata a kuruciya tare da cikakken ilimi. Mai shari’a Bello ya rasu a shekarar 1956, ya bar Adamu a hannun babban yayansa mai shari’a Aminu Bello.[ana buƙatar hujja]
Bello ya kammala digirinsa na farko a fannin tattalin arziki a Jami'ar Ahmadu Bello da ke jihar Kaduna a karamar hukumar Zaria a shekarar 1975.[ana buƙatar hujja] kuma ya kammala digirinsa na Kasuwanci (MBA) a Jami'ar Pittsburgh a shekarar 1982.[ana buƙatar hujja]Ya halarci Makarantar Kasuwancin Harvard na mako shida na Advanced Management Programme a cikin shekarar 1990.[ana buƙatar hujja]
Aikin bankinsa da yayi
gyara sasheBello ya fara aikin banki ne a shekarar 1976 a matsayin babban mai kula da harkokin zuba jari a kamfanin New Nigerian Development Company (NNDC). Tsakanin shekarar 1976 zuwa 1981, ya tashi ya zama Janar Manaja na "New-Devco Finance", reshen (NNDC). A shekara ta alif 1983 Bello ya koma Habib Bank a matsayin mataimakin Manajan Darakta, daga nan kuma ya kuma zama manajan Darakta, sannan ya zama babban darakta a shekarar 1988, ya ci gaba da rike mukamin har zuwa shekara ta alif 1994. Bayan ya bar bankin ya zama mai ba da shawara kan harkokin kudi, mai gina gidaje, kuma mai hannun jari a fannoni da dama har zuwa lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban hukumar gudanarwar "bankin Intercity" a shekarar 1998, sannan ya zama shugaban kwamitin gudanarwa. na "Habib Nigeria Bank" a shekarar 1999, inda a baya ya taba zama babban jami’in gudanarwa.
Ministan Noma da Raya Karkara
gyara sasheA watan Janairun shekarar 2001, Shugaba, Olusegun Obasanjo, ya zabi Bello a matsayin Ministan Noma da Raya Karkara na Nijeriya, kuma ya fara aiki a watan Fabrairun Shekarar 2001. Shugaba Obasanjo ya sake nada Bello ne bayan an sake zabensa a shekara ta 2003.
Bello a matsayin Minista, Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta inganta hanyoyin sadarwa tun daga yankunan karkara zuwa kasuwannin birane da samar da ruwan sha domin taimakawa noman rani, wani lokacin tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Majalisar Dinkin Duniya .
Bello shi ne Ministan Noma na Najeriya da ya fi kowane minista dadewa a mukamin.
Ministan noma da albarkatun ruwa
gyara sasheA cikin Janairu shekara ta 2007, an rage adadin ma'aikatun daga 34 zuwa 19. An kuma haɗe ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya da ma’aikatar albarkatun ruwa in da ta koma babbar ma’aikatar a gwamnatin tarayya, inda Bello ya zama ministan noma da albarkatun ruwa tare da kananan ministocinsa kwara biyu.
Rigimar da ta faru yana Minista
gyara sasheWatanni hudu bayan da Bello ya hau sabon mukaminsa na minista, ya amince da shigo miliyoyi tan na wake zuwa Najeriya daga Burkina Faso, matakin da ya sha suka sosai a kafafen yada labarai na cikin Nijeriya.
Bello ya sha zargi daga tsohon shugaban kwamitin noma na majalisar dattawan Nijeriya, wato Sanata Bode Olowoporoku in da ya zarge shi da hada baki da wasu kamfanoni na kasashen waje, wajen damfarar kasar nan kudi naira biliyan 3.4 don shigo da takin zamani na noma. Daga zarge-zargen, akwai cewar ya sayo buhun takin Naira 1500 a kasar Ukraine, wadda ita ce kasar da tafi shigowa da taki Nijeriya, amma ana zargin ministan da sayar da takin kan Naira 2800 tare da cewar duk kudin da aka dora na ministan ne. Amma Bello ya shaidawa majalisar ministocin tarayya cewa an samu banbancin rabe-raben ne saboda sufuri da kudaden haraji da aka yi a lokacin jigilar takin daga kasar Ukraine zuwa Najeriya, wanda majalisar ta amince da hujjojinshi. Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta (EFCC) da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ne suka yi watsi da karar ta sanatan akan ministan.
Olowoporoku dai bai hakura ba ya ci gaba da shari’ar da ya ke yi da Bello, har ma ya raka karamin ministan noma, wato Bamidele Dada daga zauren majalisar dattawa a lokacin da ya zo tattaunawa akan lamarin. Bello ya ce, Olowoporoku yana yi ma sa bi ta da kulli ne saboda rashin ba shi kwangilar shigowa da takin da ake magana a kai, wanda kwangilar zai iya ba shi Naira miliyan 200. Sanatan ya musanta cewa ya taba neman kwangila daga ma’aikatar, amma bincike ya tabbatar da cewa Bello ya yi gaskiya anan, kuma majalisar ta sauke Olowoporoku daga mukaminsa na shugaban kwamitin noma tare da cire shi daga dukkan kwamitoci na majalisar dattawa. Daga karshe ma dai an kore shi daga jam'iyyar People's Democratic Party mai mulki. An yi ta yada al’amarin a kafafen yada labarai a Nijeriya.
Lakabi da nade-nade da akayi masa
gyara sasheBello ya samu sarautar “Dan Iyan Adamawa” a shekarar 1989 daga masarautar mahaifarsa ta tsohuwar jihar Gongola wato adamawa a yanzu. A shekarar 2003 kuma, ya sake samun wani mukami na sarauta; wato "Otun Babalakin" a jihar Ekiti.
Bello ya zama fellow Chartered Institute of Nigeria (FCIB) a shekarar 1991. Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola ta ba shi lambar girmamawa ta Doctorate (Honoris Causa).
An nada Bello a matsayin Commander of the Order of the Federal Republic CFR, a watan Disambar shekarar 2006, wanda shi ne mamba na farko a majalisar ministocin tarayya da aka yi wa ado ta wannan hanya. Ya kuma samu lambobin yabo na shugabanci da dama, kuma kungiyoyin yada labarai da dama a Najeriya sun zabe shi a matsayin gwarzon minista a lokacinsa.
Rayuwarsa
gyara sasheBello ya auri pharmacist Lubabatu Bello, kuma suna da ‘ya’ya shida.[ana buƙatar hujja]
Manazarta
gyara sashe
- Babatunde, Jimoh.