Sani Daura
Sani Zangon Daura An haifeshi a cikin garin karamar hukumar Zango dake a jahar Katsina, Nijeriya.Ya rike mukamin Ministan noma da raya karkara, daga baya kuma ya rike mukamin Ministan muhalli a majalisar ministocin shugaba Olusegun Obasanjo.An cire shi daga majalisar ministocin Obasanjo a cikin garambawul a ranar 30 ga Janairun 2001.[1].
Sani Daura | |||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
13 ga Yuni, 2023 - ← Ahmad Babba Kaita District: Katsina North
11 ga Yuni, 2019 - District: Zango/Baure
2000 - 30 ga Janairu, 2001 ← Hassan Adamu (en) - Mohammed Kabir Said (en) →
29 Mayu 1999 - 2000 - Hassan Adamu (en) →
| |||||||||||
Rayuwa | |||||||||||
Haihuwa | Jahar Katsina, 23 ga Janairu, 1959 (65 shekaru) | ||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||
Karatu | |||||||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||||||
Sana'a | |||||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||||
Imani | |||||||||||
Jam'iyar siyasa | Jam'iyyar National Party of Nigeria |
Bayan Fage
gyara sasheSani Zangon Daura ya fito ne daga shiyyar Daura ta Sanatan Katsina. Ya kammala makarantar koyon karatun larabci da ke Kano. Ya samu tallafin karatu don halartar Makarantar African and Oriental Studies dake Landan a 1961. Amma ya dawo Nijeriya kafin ya kammala karatun kuma ya samu shiga Jami’ar Legas . A lokacin Jamhuriya ta biyu ta Najeriya a 1979, ya kasance dan takara a zaben fidda gwani na Jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN) don yin takarar Gwamnan Jihar Kaduna, amma ya sha kaye a hannun Alhaji Lawal Kayta. Kayta shi kuma ya sha kaye a hannun dan takarar jam'iyyar Redemption Party (PRP) Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa .[2]
Matsayin hukuma
gyara sasheBayan nada shi Ministan Gona a watan Yunin 1999, Daura ya gabatar da wata manufa ga bangaren wanda a wancan lokacin ya kai kashi 38% na GDP. Manufofin sun hada da kara samarwa da kuma habaka noma, inganta noma ta hanyar fasaha, rage talauci, bunkasuwar masana'antun agro, bunkasa fitar da kayayyaki da kare muhalli.[3]
A watan Nuwamba 2000, ya kasance wakilin Najeriya a taron Majalisar Dinkin Duniya kan Canjin Yanayi da aka gudanar a Netherlands.[4] Daura ya kasance shugaban kungiyar na 77 (G77), kungiyar kasashe 133 masu tasowa da China. A wani babban jawabi a taron ya yi gargadin cewa kasashe matalauta ba za su takaita hayakin da suke fitarwa ba har sai kasashen masu arziki sun cika alkawuran da suka yi a karkashin yarjejeniyar Kyoto Protocol[5].Daura ya ce Amurka ta haifar da "annobar canjin yanayi" mai lahani kamar mulkin mallaka na Afirka.[6] Taron ya kasa cimma wani sakamako.[7]
Daga baya aiki
gyara sasheDaura ya zama mamba na kwamitin amintattu na kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), wata kungiyar masu fada a ji a Arewa. A watan Maris na 2006, yana cikin shugabannin ACF masu tsananin adawa ga barin Shugaba Obasanjo ya sake tsayawa takara a karo na uku a 2007.[8] A watan Disambar 2008, Daura ya karbi lambar yabo ta Kwamandan Umarnin Nijar (CON).[9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Akinjide Akintola (30 January 2001). "Obasanjo Sacks 10 Ministers-Sarumi, Jemibewon,Adeniran,Bunu,Sango, Others Thrown out". P.M. News. Retrieved 2010-05-06.
- ↑ NURUDDEEN M. ABDALLAH (25 October 2009). "As a student in Unilag, I saw the 1966 military coup coming - Sani Zangon Daura". Sunday Trust. Archived from the original on 8 July 2011. Retrieved 6 May 2010.
- ↑ J.Y. Maisamari. "Ways of Revamping Agro-Based Industries in the States" (PDF). Central Bank of Nigeria. Retrieved 2010-05-06.
- ↑ "Sixth Conference of the Parties to the UN Framework Convention on Climate Change". The International Institute for Sustainable Development. 23 November 2000. Archived from the original on 2012-03-09. Retrieved 2010-05-06.
- ↑ "Third World Blasts Rich Countries at UN Climate Talks". Agence France Presse. November 15, 2000. Archived from the original on March 24, 2010. Retrieved May 6, 2010.
- ↑ "More Than Just Hot Words". Los Angeles Times. November 27, 2000. Retrieved 2010-05-06.
- ↑ Julie Hyland (1 December 2000). "UN climate summit fails amid bitter recriminations between US and Europe". International Committee of the Fourth International. Retrieved 2010-05-06.
- ↑ Emeka Mamah, Rotimi Ajayi & Emmanuel Aziken (March 15, 2006). "North won't accept Obasanjo beyond 2007 -AREWA •Anti-3rd term Senators mobilise against Mantu". Vanguard. Retrieved 2010-05-06. [dead link]
- ↑ Abdullahi M. Gulloma (12 December 2008). "Gani, Service Chiefs, 271 Others Bag National Honours". Daily Trust. Retrieved 2010-05-06.