Uzee Usman Adeyemi (An haife shi a ranar 11 ga watan Nuwamba , shekarar 1986) ɗan Najeriya ne kuma Furodusa Furodusa wanda aka san shi da fim ɗin Oga Abuja. Uzee Usman ya fito ne daga jihar Kwara kuma ya girma a Kaduna, jihar Kaduna. Yana da digiri biyu a Kimiyyar Siyasa da Turanci a Jami’ar Abuja da Jami’ar Jos kafin ya ci gaba da karatun fim na Musamman a Afirka ta Kudu.

Uzee Usman
Rayuwa
Cikakken suna Uzee Usman Adeyemi
Haihuwa Jahar Kaduna, 11 Nuwamba, 1986 (37 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar, Jos : Turanci
Jami'ar Abuja : Kimiyyar siyasa
Matakin karatu Digiri
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Yarbanci
Sana'a
Sana'a darakta, mai tsara fim, jarumi da mai gabatar wa
Muhimman ayyuka Eagle Wings
Kyaututtuka
Ayyanawa daga
IMDb nm10217931
Uzee Usman

Ya fara aikinsa a 2003 a matsayin mai zane-zane, A shekarar 2013, ya tsunduma cikin shirin fim kuma ya samar da fina-finai da suka lashe kyauta, duka a cikin Kannywood da nollywood ciki har da Oga Abuja, wanda ya ci Kyakkyawan Fina-Finan Hausa na Shekarar 2013 a gasar City People Entertainment; da kuma Maja wadda ya lashe kyautar Fim mafi kyawu a shekara (Kannywood) a bikin bayar da kyaututtukan girmamawa na City People Entertainment Awards a shekarar 2014.

Manazarta

gyara sashe

https://www.dailytrust.com.ng/uzee-from-makeup-artist-to-film-director.html[permanent dead link] https://www.premiumtimesng.com/entertainment/153150-brought-john-okafor-nkem-owoh-kannywood-usman-uzee.html