Mikiya
Mikiya: ana kiranta da turanci da (Eagle) wata tsuntsuwa ce daga cikin tsuntsaye masu cin nama, sai dai wasu na gani kalmar Mikiya suna ne da ya haɗa baki ɗayan sunayen tsuntsaye masu cin naman junan su da kuma sauran dabbobi, suna kama da junan su. A taƙaice mikiya tsuntsuwa ce da take tashi sama kamar shaho itama kamar yadda shaho yake farauta haka take, sai dai ita tafi shaho hatsari don kuwa har naman mutane tana ci, musamman ƙananan yara. Akwai karin magana da hausawa keyi wai shi "Dirar Mikiya" wato anzo ba tare da an sanar ba. [1][2][3]
shaho | |
---|---|
organisms known by a particular common name (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Accipitridae (en) |
Name (en) | ɸəra |
Main food source (en) | lamb (en) |
Produced sound (en) | eagle cry (en) |
Taxon known by this common name (en) | Accipitridae (en) |
Kamar yadda nafaɗa ita Mikiya kusan tana da dangantaka da shaho da mujiya da sauransu. Masana sunce mafi yawa kaso sittin (60) na kalolin Mikiya ana samun sune a ƙasar Turawa da Afirka, bayan waɗannan yankuna ana samun kaloli daban-daban har guda 14 a Amerika da ƙasar Ostireliya. Ita Mikiya naman tsuntsaye take farauta don yin kalaci, ko da yake wani lokacin ma har mutane takan yi musu barazana musamman ƙananan yara, kamar yadda ya gaba ta.
Futunan Mikiya
gyara sasheWaɗannan wasu ne daga cikin hotunan Mikiya a sassa daban-daban.
Girman Mikiya da sifofin ta
gyara sasheMikiya tanada girma, sannan tana da ƙarfi sosai, tana da girman kai (kanta babba ne) da kuma tsinin baki wanda ya kusan kai reza kaifi, haka mikiya tana da dogwayen fuka-fukai, shiyasa take da saurin tashi da nisa a sararin samaniya, da tsinin bakinta take ɗaukan naman da ta farauto, haka kuma mikiya tana da dogwayen ƙafafu kuma murɗaɗɗu dasu ga ƙambori. Mikiya tafi dukkan sauran tsuntsaye masu cin nama ƙarfi da tsinin baki, don tana iya ɗaukar dabbar da ta kai nauyin buhun siminti (cement). Haka Mikiya tana da ƙarfin ido, har takan ɗan gani ta baya sai dai ba sosai ba, masana sun bayyana cewa idon mikiya a yayin da ta fito farauta ya fi guda biyu, ma'ana tana iya hango abinda take farauta daga waje mai nisa sosai, wato tana amfani da ƙarfin idonta don hango abin farauta daga waje mai nisan gaske. Sai dai mataye a cikin mikiya sunfi maza girma saɓanin wasu tsuntsayen. Haka mikiya tana iya ganin kifi dake cikin ruwa har ta kamo shi saboda ƙarfin idonta. [4] Mikiya tana amfani da ƙumbarta don ɗauko duk wani dabba da ta farauto.
Gidan Mikiya/Shekar Mikiya
gyara sasheMikiya kamar yadda mafi yawan tsuntsaye suke yin sheka wadda zasu zauna su yi ƙwai har su ƙyanƙyashe, itama da kanta take yin shekarta (gidanta) don yin ƙwai. Sai dai na mikiya yasha banban da sauran tsuntsaye saboda ita tana neman dogayen itace masu tsawo sosai, da kuma masu ruƙuƙi masu wahalar hawa ballantana ma akai ga ƙwayayenta. Mafi yawan ƙwayayen mikiya basa wuce ƙwai biyu, wasu masana sunce tun a ƙwai ake gane na maza da mata don na mata yafi na maza girma. Sai dai mikiya tana haɗuwa da cikas a yayin da take ƙyanƙyasa daga wajen ƴan'uwanta don suna barazanar cinye ƴa'ƴan da ta ƙyanƙyansa jariran, wani lokacin ma har su kai ga sun cinye su.
Mikiya biyar mafi girma a duniya
gyara sashe- Mikiya ruwa (Steller's sea eagle. scientific name, Haliaeetus pelagicus) wadda nauyin ta ya kai 6.97kg
- Mikiyar pilipinis (Philippines eagle. Scientific name, pithecopaga jefferyi) wadda nauyin ya kai 6.35kg
- Babbar Mikiya (Harpy eagle. Scientific name, harpia harpyja) wadda nauyin ta ya kai 5.95kg
- Mikiya mai farar wutsiya (Hwute-tailed eagle. Scientific name, Haliaeetus albicilla) wadda nauyin ta ya kai 4.8kg
- Mikiya mai ƙambi (Crowned eagle. Scientific name, polemactus bellicosus) wadda nauyin ta ya kai 4.6kg.
Kashi-kashi na Mikiya
gyara sasheMikiya ta kasu kashi huɗu
- Mikiyar macijiya (Snake eagle)
- Mikiyar kifi (fish eagle)
- Ƙatuwar Mikiya ta kurmi (giant forest eagle)
- Mikiya ta gaskiya (true/booted eagle)
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Mikiya ta kashe wani yaro a Somaliya". bbc hausa. 13 September 2019. Retrieved 13 July 2021.
- ↑ Gambo Ahmad, Abdurrahman (20 August 2019). "EFCC ta yi wa gidan tsohon Gwamnan Lagos dirar mikiya". rfi hausa. Retrieved 15 July 2021.
- ↑ Briggs, Helen (30 June 2021). "Amazon eagle faces starvation in 'last stronghold'". bbc news. Retrieved 15 July 2021.
- ↑ Harande, Yusuf (13 June 2016). "Mikiya "Eagle" Da Yunkurin Satar Dan Mutun!". dandalin voa. Retrieved 13 July 2021.