Aljannah
Aljannah; Wani ni'imtaccen muhalline da Allah yayi tanadinsa ga bayinsa (mutane da aljanu) wadanda sukai biyayya a gareshi, a cikin wannan rayuwar ta duniya. Sannan ana haduwa da wannan ni'imtaccen muhallin ne a bayan wannan rayuwa ta duniya ta Kare, wato za'a fara haduwa da wannan ni'imar ta Aljannah ne tun daga farkon rayuwar kabari har ya zuwa lokacin da za ai ma bayi hisabi (Tashin Alkiyama).
Aljannah | |
---|---|
Garden of Eden (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | mythical location (en) da otherworld (en) |
Hannun riga da | wuta |
Aljannah cike take da
lambuna da koramai da
idanuwan ruwa masu dadi
wacce bamai zartsiba akwai
farantai na zinare da lu'ulu'u da kuma gadaje na ni'ima da tufafi na alhariri koraye. Aljannah tana da hawa hawa
kololuwarta ita ce Jannatul Firdausi.
Allah madaukakin sarki
yace lallai masu takawa suna acikin gidajen aljannah mai
idanuwan ruwa (46) kushigeta
da aminci, kuna amintattu(47)
kuma muka debe abinda ke cikin zukantansu na kyashi, (suna masu zama) 'yan uwan juna, suna kishingida cikin fuskantan juna akan gadaje (48).