Sheikh Shi'itu Ghali
Imam Shi'ithu Ghali Kadawa shi ne Sarkin Madina Malamai na biyu, Jagoran Ruhaniya kuma limamin Kadawa, Warawa, an haife shi a gidan Banu Gha mai daraja kuma dan kabilar Madina ne, Majalisar Masarautar Kano ta naɗa shi bayan rasuwar mahaifinsa Imam Ghali.[1][2][3][4][5][6][7][8][9]
Sheikh Shi'itu Ghali | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a |
Tarihin shi
gyara sasheImam Shi'itu Ghali ya taka rawar gani wajen tabbatar da Addinin Musulunci a Masarautar Kano, wasu daga cikin iyalansa sun yi ikirarin cewa su Sharifawa ne kuma sun samo asali ne daga Annabi Muhammad (S A W), sun ce zuriyar Banu Hashim na ƙuraishawa ne, ta hanyar Sharif ibn Ali, Hasan. ibn Ali ɗan Aliyu bn Abi Ɗalib da Annabi Muhammad (S A W), zuriyarsa suna kiran kansu Larabawa, Fulani, Hausawa, Larabawa Hausa-Fulani dangane da al’adunsu, ana kiransu Madinawa Malamai dangane daga birnin Madina. suna da'awar cewa sun samo asali ne daga, da'awar zuriya daga ƙabilar Larabawa da Annabi ta zama ruwan dare a zuriyar malamai a fadin Arewacin Najeriya da Sahara.[10][11][12][13]
Tarihin Sarauta
gyara sasheShi ne Sarkin Madinawa an naɗa shi Limami kuma Jagoran Ruhi a Kadawa, Warawa ta Masarautar Kano, a lokacin da yake Limami ya ci gaba da ɗabbaƙa Mazhabar Malikiyya a Masarautar ta hanyar yin tasiri ga malamai daga baya.[14] an yi amfani da tsarin mazhabar Malikiyya maimakon sauran mazahabobin Musulunci, mazhabar Malikiyya ɗaya ce daga cikin manya-manyan mazhabobi hudu na fikihu a cikin Musulunci gun Ahlus Sunna.[15] Malik bn Anas ne ya assasa ta a ƙarni na 8. Mazhabar Malikiyya ta dogara ne da Alqur'ani da Hadisi a matsayin hujja ko madogara ta farko. Ba kamar sauran malaman fiqhu na Musulunci ba, shi ma Malikiyya fiqhu yana ganin ijma’in mutanen Madina a matsayin sahihiyar tushen shari’ar Musulunci, mazhabar Malikiyya daya ce daga cikin manya-manyan kungiyoyin Musulmi ƴan Sunna, kwatankwacin mazhabar Imam Shafi’i a mabiya, amma kadan ne, fiye da mazhabar Imam Hanafiyya. Shari'a bisa koyarwar Maliki ana samun rinjaye a Arewacin Afirka (ban da arewa da gabashin Masar), Afirka ta yamma, Chadi, Sudan, Kuwait, Bahrain, Masarautar (UAE), da kuma a arewa maso gabashin Saudi Arabia. Littattafan tarihi ya ruwaito cewa ya kasance mai zuhudu sosai (wato gudun duniya). A Masarautar Kano wasu suna kallonsa a matsayin Waliyi, da ya yi wafati an binne shi a Kadawa, babu wani tarihin ranar rasuwarsa a cikin littattafan tarihin Masarautar.[16] Imam Shi’itu, yanada da ra’ayin da togewa akan cewa, lallai wajibi ne musulmi su yi imani da shika-shikan Musulunci guda biyar, a cikin dukkan Annabawan Musulunci tun daga Adamu har zuwa Annabi Muhammad (S A W) da mala’iku, ya kuma yi imani da sifofin Allah da suka keɓanta da shi kamar samuwa/Na farkon da da ba'a san farkon sa ba (Allah). dawwamamme da bayada ƙarshe, na ƙarshe mara ƙarshe, kuma wanda ake da buƙata a gare shi yayin da ba shi da buƙata a gun kowa. Ma buwayin da babu wanda ya sha gabansa, shi kaɗai yake bayada abokin tarayya a cikin gudanar da mulkin sa, rayayyen da baya mutuwa, gyangyaɗi bai ɗauke shi ba ballantana bacci, wanda bayi kamanceceniya da abubuwan halitta ba, Kaɗaita Allah, da kuma tabbatar da Allah mai iko ne akan komai, ma ƙagin komai da komai, ma sani, mai gani ba irin ganinmu na halitta ba, mai ji ba irin jinmu ba, mai magana da dai sauran Tauhidin kaɗaita Allah mabuwayi. A halin yanzu zuriyarsa da mabiyansa sun kasu zuwa ƙungiyar Izala, Qadiriya da Tijjaniyya duk da cewa Tijjaniyya suke da rinjaye a cikin zuriyarsa yayin da wasu kaɗan ba su da ɗarika. Ɗaya daga cikin limaman masallacin Kadawa na ƙaramar hukumar Warawa Sheikh Usaini Umar (Malam Bala) shi ne zuriyarsa. Daularsa ta yi tasiri a Masarautar Kano bayan yaƙin basasar Kano wanda aka yi da fitowar Aliyu Babba a matsayin Sarkin Kano. Masarautar ta samar da limamai da dama da malaman tauhidi da masu riƙe da mukaman gargajiya da masu rike da mukaman gwamnati da ƴan siyasa a Daular Sakkwato.[17][18]
A Masarautar Kano ana kiran zuriyarsa da waliyyai da larabci (أولياء) Awliya Madinawa Malamai, dangane da birnin Madina da suka ce sun fito, da ke yammacin Saudiyya kuma mafi yawan kakanninsu waliyyai ne. Zuriyarsa waɗanda suke zuriyar Jobawa ta ɓangaren uwa, wani da aka naɗa shi a matsayin Makaman Kano saboda cancanta sa, da kuma fifikon da aka nuna a zamanin Sarkin Kano Aliyu Babba, wanda ya naɗa Sarkin Takai Umaru Dan Maisaje a matsayin Makaman Kano, wanda alaƙarsa da shi take da kyau. Jobawa ta hannun mahaifiyar sa Habiba, ƙanwar Malam Bakatsine, ba a yi la'akari da bukatu na zuriya ta al'ada ba wajen naɗin da ya kai ga samar da fifiko ga zuriyar Jobawa mai alaƙa ta uba ko uwa uba da burin a naɗa, a matsayin Makaman Kano.[19][20]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Bashir, Ali (2000). Kano Malams in the Ninteenth Century. River Front Press.
- ↑ Hassan, Mohammed (2018). Islamic Religious Practices and Culture of the Al-Ghali Family. Tafida Printing Press.
- ↑ Abubakar, Badamasi. Trans Saharan Trade: Networks and Learning in Ninetenth Century Kano. Danjuma Press.
- ↑ Aminu, Muhammad. The History of Al-Ghali Family. Gargaliya Press.
- ↑ Sani, Muhammadu (1990). Arab Settlers in Kano. Sauda Voyager.
- ↑ Balogun, Ismail A.B (1969). The penetration of Islam into Nigeria. Khartoum: University of Khartoum,Sudan, Research Unit.
- ↑ Danlami, Yusuf (2005). Al-Ghali Family and its Religious Leaders. Danlami Printers.
- ↑ Tarikh Arab Hadha al-balad el-Musamma Kano. Journal of Royal History. 1908.
- ↑ Balarabe, Suleman (1987). The History of Kadawa Town. Bala Printing Press.
- ↑ Abdullahi, Ahmed (1999). Madinawan Kano. Kano: Danlami Printers.
- ↑ Norris, H.T. (1975). The Tuaregs:Their Islamic Legacy and Its Diffusion in the Sahel. England: Aris and Phillips,Ltd.
- ↑ Last, Murray (1967). The Sokoto Caliphate. New York: Humanities Press.
- ↑ Bello, Ahmadu (1962). My Life. Cambridge University Press.
- ↑ Santali, Muhammadu (1981). The Kadawa Imams. River Front Press.
- ↑ Abdullahi, Ahmed (2004). Maliki School of thought in the Kano Emirate. River Front Press.
- ↑ Ramadan, Hisham M. (2006). Understanding Islamic Law: From Classical to Contemporary. Rowman Altamira. pp. 26–27. ISBN 978-0-7591-0991-9.
- ↑ Larkin, Barbara (July 2001). International Religious Freedom (2000). ISBN 9780756712297.
- ↑ Jurisprudence and Law – Islam Reorienting the Veil, University of North Carolina (2009)
- ↑ Smith, M.G. (1997). Government in Kano 1350-1950. Westview Press, A Division of HarperCollins Publishers, Inc.
- ↑ Abdullahi, Ahmed (1998). Tarihin Madinawa Jobawa. Kadawa Press.