Sani Abdullahi Shinkafi, ɗan siyasan Nijeriya ne kuma mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin gwamnatocin jihar Zamfara, Bello Matawalle . Ya taba zama sakatare na kasa na All Progressives Grand Alliance .

Sani Abdullahi Shinkafi
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Jihar Nasarawa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Shinkafi a garin Shinkafi, karamar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara. Daga shekara ta 1976 zuwa shekara ta 1982, ya tafi makarantar firamare ta garin Shinkafi, a jihar Zamfara, kafin ya wuce makarantar sakandaren gwamnati, Gwadabawa, jihar Sokoto inda ya yi karatu daga shekara ta 1982 zuwa shekara ta 1988. Ya tafi Makarantar Fasaha ta Sakkwato sannan daga baya ya wuce Makarantar Nazarin Gudanarwa, Birnin Kebbi, Jihar Kebbi a cikin shekara ta 1991 kuma ya sami difloma ta kasa a harkokin kasuwanci. A shekara ta 1998, Shinkafi ya sami babbar difloma ta kasa a fannin lissafi da kudi daga Makarantar Akawu da Karatu ta Jos, Jos. Ya samu difloma a fannin ilimi a kwalejin koyar da malamai ta kasa, a jihar Kaduna a shekara ta 2008, kafin ya samu digiri na biyu a bangaren ayyukan gwamnati daga Jami’ar Jihar Nasarawa.[1]

Shinkafi ya fara aikin sa ne ta hanyar yin aiki tare da gwamnatin jihar Sakkwato a matsayin akawun wajen horarwa da ma'aikatar noma da albarkatun kasa a jihar. A shekara ta 1992, ya samu karin girma zuwa mai binciken ciki na II sannan daga baya aka mayar dashi kamfanin gine-gine na jihar Sakkwato inda ya yi aiki a matsayin mukaddashin daraktan riko, odit na ciki. Bayan kirkirar jihar Zamfara, sai aka mayar da shi ma'aikatar kudi, kasafi da tsara tattalin arziki a jihar.[2][3][4] A shekara ta 2001, bisa radin kansa ya yi murabus daga mukamin nasa ya koma kamfanoni masu zaman kansu.

Daga baya Shinkafi ya shiga siyasa sannan ya zama dan takarar gwamna na jam'iyar All Progressives Grand Alliance a zabukan gwamnoni na shekara ta 2007, da shekara ta 2011, da shekara ta 2015 da kuma shekara ta 2019 a jihar Zamfara. A cikin shekara ta 2015, ya zo na uku a zaben gwamnan da ya ga Abdul'aziz Abubakar Yari ya sake zaba a karo na biyu kuma na karshe. A shekara ta 2019, ya zo na hudu a zaben gwamna. Shine shugaban yanzu na kungiyar Patriots for Advancement of Peace and Social Development, (PAPSD). Shinkafi tsohon sakataren jam’iyyar All Progressives Grand Alliance na kasa kuma sakatare a yanzu na kwamitin amintattu na jam’iyyar.

A watan Yunin shekara ta 2020, an naɗa shi mai ba da shawara na musamman na girmamawa kan harkokin gwamnatoci ga gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle. Har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin mai ba shi shawara na musamman, ya kasance mamba a kwamitin jihar Zamfara don gano bakin zaren rikicin 'yan bindiga da gwamna Matawalle ya kirkiro don magance rashin tsaro a jihar.[5][6]

Manazarta

gyara sashe
  1. Wuyo, Ibrahim Hassan (10 June 2020). "Matawalle appoints Sani Abdullahi, former APGA scribe as Special Adviser". Vanguard Newspaper. Retrieved 26 December 2020.
  2. Umar, Shehu (10 February 2019). "As Uncertainty Dogs Zamfara APC: Mutawalle, Dansadau, Shinkafi, Adamu Fight For Guber Seat". Daily Trust Newspaper. Retrieved 26 December 2020.
  3. Mohammed, Munirat Nasir (4 March 2015). "Zamfara: Would incumbency factor play out?". Blueprint Newspaper. Retrieved 26 December 2020.
  4. Ezigbo, Onyebuchi (1 March 2019). "Zamfara APGA Guber Candidate Petitions INEC over REC, CP". This Day Newspaper. Retrieved 26 December 2020.
  5. Jimoh, Abbas (25 June 2020). "Why I Accepted Gov Matawalle's Appointment – Shinkafi". Daily Trust Newspaper. Retrieved 26 December 2020.
  6. "Ex-IGP heads panel to proffer solution to banditry in Zamfara". The Nation Newspaper. 10 July 2020. Retrieved 26 December 2020.