This Day

Jaridar ƙasa ta Najeriya

Jaridar This Day Jarida ce ta ƙasar Najeriya. Ita ce babbar jaridar kamfanin, Leaders & Company Ltd kuma an fara buga ta a ranar 22 ga watan Janairu 1995. Hedikwatar ta na a Apapa, jihar Legas.[1] Nduka Obaigbena, shugaba kuma babban editan ƙungiyar This Day Media Group da Arise News ne ya kafa ta.

This Day
Bayanai
Suna a hukumance
This Day
Iri takardar jarida
Ƙasa Najeriya
Ƙaramar kamfani na
Harshen amfani Turanci
Mulki
Hedkwata Lagos,
Mamallaki Nduka Obaigbena
Tarihi
Ƙirƙira 1995

thisdaylive.com


this day
This day
This Day

This Day memba ce ta Kamfanin Dillancin Labarai na Belt and Road.[2] Tun daga shekarar 2014, ta ci gaba da ƙulla alaƙa da ofishin jakadancin ƙasar Sin.[3]

A baya dai an soki mawallafin jaridar This Day Nduka Obaigbena da rashin biyan ma’aikatan jaridar da kuma masu kawo kayayyaki.[4]

Hare-hare da ƙalubale

gyara sashe

A shekarar 2001, wasu editoci da dama sun tsallake rijiya da baya a wani hatsarin jirgin sama a filin jirgin Maiduguri da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.[5][6]

A shekarar 2012 ne aka kai wa, wa su ofisoshin Jaridar harin bom a cikin mota, a Abuja babban birnin ƙasar, da kuma Kaduna, harin ƙuna baƙin wake da aka kai da wasu motoci da ake kyautata zaton ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram ce ke da alhakin kai Hara-haren.[7][8]

Wanda ya kafa jaridar, Nduka Obaigbena ya yi gudun hijira a Landan a shekarar 1998, kafin ya dawo Najeriya.[9]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. "About Us - thisdaylive". This Day (in Turanci). Retrieved 2018-04-26.
  2. "Adeniyi Joins Chinese Belt and Road Media Council – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2023-01-29.
  3. Batchelor, Kathryn; Zhang, Xiaoling, eds. (2017-06-26). "Newspaper coverage of China's engagement with Nigeria: Partner or predator?". China-Africa Relations: Building Images through Cultural Cooperation, Media Representation and Communication (in Turanci) (1 ed.). Routledge. doi:10.4324/9781315229096-10. ISBN 978-1-315-22909-6.
  4. Jon Gambrell (10 May 2013). "Newspaper Staffers Strike Against Publisher Nduka Obaigbena In Nigeria". The Huffington Post. AP. Archived from the original on 2 March 2015. Retrieved 1 March 2015.
  5. "Nigeria: This Day Editors In Plane Crash". allAfrica.com. P.M. News. 24 January 2001. Retrieved 6 July 2020.[dead link]
  6. Odusile, Waheed; Umar-Omale, Peter (26 January 2001). "Nigeria: Maiduguri Plane Crash: IBB, Ibori, Afenifere, Others Greet THISDAY". allAfrica.com. THISDAY. Retrieved 6 July 2020.[dead link]
  7. "Nigeria's ThisDay newspaper hit by Abuja and Kaduna blasts". BBC News. 26 April 2012. Archived from the original on 26 September 2016. Retrieved 6 July 2020.
  8. Eboh, Camillus; Mohammed, Garba (26 April 2012). "Suicide car bombs hit Nigerian newspaper offices". Reuters. Archived from the original on 6 July 2020. Retrieved 6 July 2020.
  9. "Tributes to Olusegun Osoba and Nduka Obaigbena". THISDAY. 13 July 2019. Archived from the original on 23 August 2019. Retrieved 6 July 2020.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe