Mutanen Marghi

al'ummar Najeriya, Kamaru da Cadi

Al'ummar Marghi ( Margi ) ƙabila ce a Najeriya, galibi suna zaune a jihohin Adamawa (Askira) da Borno (Askira Uba) . Suna da yawan jama'a da aka kiyasta adadin 360,000 kuma suna sadarwa ta amfani da yaren Marghi . Duk da cewa suna da nasu yare, mutanen Marghi galibi suna jin harsuna biyu, wani lokacin har ma da harsuna uku. A Borno suna jin Kanuri, yayin da a Adamawa suke jin Fulfulde, duka harsunan da suka mamaye jihohinsu.  : 271-274  : 213-216 

Mutanen Marghi
Jimlar yawan jama'a
5,000,000
Yankuna masu yawan jama'a
Kameru, Cadi da Najeriya
Wani daji a kasar Marghi
Ƙauyen Margunawa (1860)

Asalin Marghi

gyara sashe

An yi ittifaki cewa mutanen Marghi sun yi hijira ne daga tsaunin Mandara da wasu tsaunuka a arewacin Kamaru . Hijirar tasu ta kasance da ƙungiyoyi na yarika daban daban, yayin da suka yi hijira cikin ƙungiyoyi ko dangi ( fal a Marghi ). Mafi yawansu sun zauna a daular Borno, yayin da wasu daga cikinsu suka yi hijira zuwa yankin Adamawa . Sakamakon zaman da suka yi a yankuna daban-daban, al'ummar Marghi sun yi tasiri wajen kawo tasiri wa al'adu daban-daban daga kabilun makwabta, irin su Kanuri, Kilba, da Pabir (Babur).  : 45-61 

Shahararrun mutanen Marghi

gyara sashe

Karin Bayani

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe