Daular Kanem–Bornu ta kasance daula ce data taɓa kasancewa wurin da a inda ayau nan ne ƙasar Cadi da Nijeriya. Masanan ƙasashe larabawa suna kiran daular da Kanem Empire daga ƙarni na 9th har zuwa sanda takasance daular musulunci Bornu (Daular Bornu) a Shekarar 1900. Kanem Empire CE tun daga shekara ta (c. 700 zuwa 1380) takasance ne ƙasashen Chad, Nigeria da Libya.[1] A matuƙar girmar daular ta tattara ƙasashe ba kawai ɗaukacin ƙasar Chad ba, takai har zuwa kudancin ƙasar Libya (Fezzan) da gabashin Nijar, arewa maso gabas din Nigeria da arewacin kamerun. A yayin da Daular Bornu take a shekara ta (1380s zuwa 1893) takasance a inda ake kira ayau arewa maso gabashin Nigeria, wanda tacigaba da girma fiye da daular Kanem, ta tattari kasashen da ayau sune ko kuma suke daga cikin kasashe kamar Chad, Nijar, Sudan, da Cameroon; an samar da’ita daga shekara ta 1380s zuwa shekarar 1893. Farkon tarihin daular an santa ne da jerin masu sarautar ko Girgam matafiyin bincike dan kasar jamus wato Heinrich Barth wanda aka gano a shekarar 1851.

Daular Kanem-Bornu

Wuri

Babban birni Njimi
Yawan mutane
Harshen gwamnati harsunan sahara
Bayanan tarihi
Mabiyi Kanem Empire (en) Fassara
Ƙirƙira 11 century
Rushewa 22 ga Afirilu, 1900
Tutar daular Kanem Bornu

Nazari akan Kafuwar Daular

gyara sashe

Kanem takasance a kudancin dake yankin kasuwanci da ake kira wato trans-Saharan trade dake tsakanin garin Tripoli da kuma yankin tabkin Cadi. Baccin mutanen biranen kasar kawai ta tattari harda wasu kungiyoyin al'ummu makiyaya masu amfani da harsuna kamar harshen Teda–harshen Daza (Toubou).

Kafuwar yankin daga Yan'cirani c. 600 BC

gyara sashe

Yadda aka Samu Kanem nada rudani. Wasu tsoffin tarihai sun danganta samuwar Kanem-Bornu da kifewar daular Assyrian Empire c. 600 BC har zuwa arewa maso gabashin tabkin Cadi.[2] amma sai dai nazarcen zamani na goyon bayan cewar samuwar yankin yafi kusanci da shigowar yanciranin.[3]

Samuwar ta daga yan Kanembu (Dugua) c. 700 AD

gyara sashe

Daga wani nazarin daya karbu, ansamu cewar masarautar tafara kafuwa ne a shekara ta 700 AD a karkashin makiyayan masu amfani da harshen Tebu-Kanembu. Ance mutanen Kanembu an tursasa sune sukabar yankunansu har zuwa kasar noma dake yankin kudu maso yammacin tabkin Chadi daga matsin siyasa da desiccation a tsohuwar mazauninsu, yankin nada yancin kanta tun asali, walled city-states belonging to the Sao culture. A karkashin mulkin Duguwa dynasty, Kanembu sun mamaye Sao, bawai bayan sun dauki aladun matanen ba.[4] ancigaba da gwabza yaki tsakanin su har zuwa karshen karni na goma sha shida (16th).

Samuwar Agisymba

gyara sashe

Wani nazarin ya nuna cewar batacciyar kasar Agisymba wanda (Ptolemy ya ambata tun a tsakiyar karni na biyu (2nd) AD) itama mafiriyar daular Kanem din ce.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kanem-Bornu". Encyclopædia Britannica. Retrieved 24 September 2014.
  2. Lange, Dierk. Founding of Kanem, 31–38.
  3. An overview of these discussions are gathered in the web page of the German scholar Dierk Lange, author of this theory: Reviews of Dierk Lange – Ancient Kingdoms of West Africa
  4. Urvoy, Empire, 3–35; Trimingham, History, 104–111.
  5. "The Mune as the Ark of the Covenant between Duguwa (Kanembu) and Sefuwa (Kanembu - Mayi)" Borno Museum Society Newsletter 66–67 (2006), 15–25. (The article has a map (page 6) of the ancient Central Sahara and proposes to identify Agisymba of 100 CE with the early Kanem state).