Mohamed Juldeh Jalloh
Mohamed Juldeh Jalloh, ɗan siyasan Saliyo ne kuma Mataimakin Shugaban Saliyo na yanzu tun daga 4 Afrilun shekarar 2018. Jalloh masanin kimiyyar siyasa ne, ɗan kasuwa kuma tsohon jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya.[1] Jalloh babban jigo ne a Jam’iyyar Mutanen Saliyo.
Mohamed Juldeh Jalloh | |||
---|---|---|---|
4 ga Afirilu, 2018 - ga Yuli, 2023 ← Victor Bockarie Foh (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Koidu (en) , 1970 (53/54 shekaru) | ||
ƙasa | Saliyo | ||
Mazauni | Freetown | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of Bordeaux (en) Jami'ar Ibadan | ||
Thesis director | Dominique Darbon (en) | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | political scientist (en) da ɗan siyasa | ||
Employers | Majalisar Ɗinkin Duniya | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa | Sierra Leone People's Party (en) |
Karatu
gyara sasheDokta Juldeh Jalloh ta samu digiri na farko a fannin kimiyyar siyasa daga Kwalejin Fourah Bay, sannan kuma ta yi digiri na biyu a kimiyyar siyasa daga Jami’ar Ibadan da ke Ibadan, Najeriya ; da digirin digirgir daga jami’ar Bordeaux a Bordeaux, Faransa.[1] Jalloh ya kware a cikin harsuna da yawa ciki har da Ingilishi da Faransanci.
Siyasa
gyara sasheJalloh masanin kimiyyar siyasa ne ta hanyar sana'a, ya fara aiki da Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2000, lokacin da yake jami'in shirye-shirye a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Kosovo . Ya kuma taɓa zama memba a kwamitin manyan masu ba da shawara a ofishin tabbatar da sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya a Mali da yankin Sahel.
An naɗa shi a matsayin abokin takarar shugaban ƙasa na Julius Maada Bio a babban zaben ƙasar Saliyo na shekarar 2018,[2] wanda suka lashe a zagaye na biyu.[3]
Rayuwa
gyara sasheJuldeh Jalloh Musulmi ne mai ibada, sannan kuma an haife shi kuma ya girma a Koidu, Gundumar Kono a gabashin Saliyo. Shi dan kabilar Fula ne.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "SLPP Mohamed Juldeh Jalloh Has A Track Record Of Achievements". SLPP Today.
- ↑ Abdul Rashid Thomas (January 10, 2018). "Bio appoints Dr. Mohamed Juldeh Jalloh as his presidential running mate". The Sierra Leone Telegraph.
- ↑ "Sierra Leone election: Julius Maada Bio fast-tracks presidential oath in a hotel". BBC. April 5, 2018.