Safa da Marwa
الصّفا, Aṣ-Ṣafā) da (المروا, Al-marwa) wasu ƙananan tsaunuka ne da suke a Babban Masallacin Makkah a Saudi Arabia da ake masa laƙabi da suna Masjid Al-Haram. Musulmai na kaiwa da dawowa sau bakwai a tsakanin su lokacin aikin Hajji da Umrah. Sun kasance a tsakiyar birnin Makkah, kewaye da gidajen mazauna birnin, tare da Dar al-Arqam. Yin gudanarwan aikin yasamo asali ne tun daga lokacin jahiliyyan larabawa kafin zuwan musulunci, waɗanda suka yarda da cewa As-Safa da Al-Marwah wasu masoya ne guda biyu waɗanda ubangijinnin suka narkar dasu saboda aikawa zina kamar yadda aka rawaito su a a hadith da dama. Al'adar zagaye As-Safa da al-Marwah ansanya shi acikin ayyukan aikin hajji tareda wasu ayyukan da suka kasance ana aikata su kafin zuwan musulunci.[1]
Safa da Marwa | ||||
---|---|---|---|---|
religious behaviour (en) | ||||
Bayanai | ||||
Bangare na | Aikin Hajji da Sa'yee (en) | |||
Ƙasa | Saudi Arebiya | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Saudi Arebiya | |||
Province of Saudi Arabia (en) | yankin Makka | |||
Tourist attraction (en) | Makkah |
Hotuna
gyara sashe-
Cincirindon Mahajjata a yayin gudanar da Ibadar
-
Dutsin Al-Marwah
Manazarta
gyara sashe- ↑ Al-Bukhari, Muhammad (846). Sahih of al-Bukhari, Vol. 2. p. 195.