Masallaci

Gurin yin Ibadar mabiya Addinin Musulinci

Masallaci jam'i, ko Masallatai: wajene da musulmai ke bautan Allah (SWA) shikadai Ubangiji kowa da kowa.[1] Da Larabci ana cewa Masjid. A wajen akasarin Musulmai, masallaci ya wuce wajen bautan Allah kadai. Musulmai na bauta tareda koyo da koyar da ilimin addinin musulunci tare da tattaunawa akan matsalolin musulmai tare da neman hanyar warware su a masallaci. A Birtaniya masallatai ne cibiyar matattarar al'umar musulmai tare da koyar da addinin musulunci. Anayin bukukuwa da taruka a masallaci, musamman ma shagulgulan daurin aure. Akwai dokokin yadda mutane zasu kasance a masallaci. Daya daga cikin su shine wani bazai takura ma wanda yake bauta ba. Masallatan farko an bude su ne a karni na 7 a fili, amma daga baya an koma ana gina masallatai a salon gini na musulunci. Masallatan Quba da Masallacin Annabi na a farko farkon masallatai. Akwai masallatai a kowacce Nahiya in banda ta Antarctica.

masallaci
building type (en) Fassara da Karatun Gine-gine
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na wajen bauta, religious building (en) Fassara da architectural structure (en) Fassara
Facet of (en) Fassara sacred architecture (en) Fassara
Addini Musulunci
Abubuwan da aka hana a wajen please take off your shoes (en) Fassara
Harabar babban masallaici
Masallacin dalhi
Masallacin kasa mai tsarki
kofar masallacin annabi
Masallacin manzon Allah

Hotuna gyara sashe

Ana gina masallatai ne a yanayin gine gine irin na musulunci a bisa akasari, amma kuma yawancin salon ginin masallatai ya danganta ne ga irin yadda salon ginin kasashe da al'adun mutane.

Manazarta gyara sashe

  1. Books, Cgp (2009). GCSE Religion Studies: Complete Revision and Practice (Revised ed.). Coordination Group Publications. p. 96. ISBN 978-1-84762-406-2. line feed character in |publisher= at position 19 (help); line feed character in |title= at position 5 (help)