Mamman Shata

mawakin gargajiya a kasar Hausa Najeriya
(an turo daga Mahaman Shata)

Alhaji Mamman ShataAbout this soundMamman Shata , ya kuma rasu a shekara ta alif dari tara da chasa'in da takwas (1998), yana da shekara fiye da 70 a lokacin da ya bar duniya (rasu). Mamman Shata yana daya daga cikin Manyan mawakan gargajiyar da aka fi sani a kasashen Hausa da ma Afirka, kai har ma da duniya baki daya. Ya kasance mashahurin Mawaki, domin a fagen wakarsa ya shahara, Kasancewarsa a cikin wakar ba abin da ba zai iya yi wa waka ba idan ya ga dama.

Mamman Shata
Rayuwa
Haihuwa Jahar Katsina, 1923
ƙasa Najeriya
Mutuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, 9 ga Yuni, 1999
Karatu
Makaranta Makarantun Musulunci da Rassansu
Harsuna Hausa
Sana'a
Artistic movement griot music (en) Fassara

" 'Yan Arewa Ku Bar Barci " na daya daga cikin wakokinsa.

Shata: 'Yan Arewa Ku Bar Barci, Najeriyarmu Akwai Dadi 'Yan Arewa a bar barci, Najeriyarmu akwai dadi. To!

'Yan Amshi: A a, 'Yan Arewa, a bar barci, Najeriyarmu, akwai dadi.

Shata: Kasar Afruka, bakar fata, Kasar Afruka, bakar fata, In ka yi yawo ciki nata. Duk ba kaman Najeriya, gidan dadi, Najeriya kasar farin jini, Najeriya ce gidan dadi, Balle Arewa uwar dadi. To!

'Yan Amshi: A a, 'Yan Arewa a bar barci, Najeriyarmu, akwai dadi.

Mamman Shata Wani shahararren mawakin Hausa ne. Haifaffen garin Musawa ne ta Jihar Katsina, amma ya yi kaura zuwa birnin Kano. Lokacin da ya rasu an yi masa sutura, aka rufe shi a garin Daura kamar yadda ya bar wasiyya. Yana da wakoki wanda bincike har yanzu bai san yawan su ba, dan shi kansa an tambaye shi ko ya san adadin wakokin da ya yi sai ya amsa da cewa bai sani ba, amma a shekarun baya an sami wata Baturiya ta zo ta hada wakokinsa kimanin dubu hudu (4,000). Yana da abin mamaki kwarai da gaske, yakan yi waka duk lokacin da aka nemi ya yi, hakan ba tare da inda-inda ba.

An tambayi Marigayi Dr Mamman Shata cewar, a ina ya soma waka sai ya kada baki ya ce “A nan Musawa inda aka haife ni a nan na soma waka kuma duk inda na je yawo to da wakata suka ganni. "

Ko wane dalili ya sa Dr Mamman Shata ya soma waka a rayuwarsa, ga dai amsar da ya bayar “Dalili shi ne kiriniya ta yarinta kurum, ba wai don gadon uwa ko uba ba, domin kuwa na dade ina yi bana karbar ko anini, in ma an samu kudi sai dai makada da maroka su dauka. Sai daga baya, bayan na mai da waka sana’a, na fara amsar kudi.

Shin waya sa wa Dr Mamman Shata wannan suna nasa wato Shata?

“Wanda ya sa mini wannan suna Shata sunansa Magaji Salam, shi ne ya samin suna Shata Mijin mai daki, ita mai dakin kaka ta ce, ita ce ta haifi wanda ya haife ni."

Da aka tambayi Dr Shata cewar wace waka ce ta fi suna kuma ya fi jin dadin ta, ko kuma ta fi birge shi a duk ilahirin wakokin da ya yi, sai ya bayar da amsa kamar haka.“ To, wannan wani abu ne mai wuyar gaske a wurina kuma kowa ya ce zai iya ganewa karya yake yi tunda shi Shatan bai gane ba „

Bisa al’ada ga yanda mawakan Hausa suke yin wakokinsu, akwai waka da suke yi wa kansu da kansu kirari a cikinta wadda aka fi sani da suna Bakandamiya. To shi ma Marigayi Dr. Mamman Shata bai yi kasa a gwiwa ba wajen yi wa kansa irin wannan waka.

Daya daga cikin hikimomin da Allah ya baiwa Marigayin Dr. Mamman Shata shi ne cewar yana iya kirkirar waka a duk lokacin da ya ga dama ko kuma aka bukaci da ya yi hakan. Misali, wakar da ya yi ta Dajin-runhu da kuma wakar da ya yi ta Canada Centre a lokacin da ya kai ziyara kasar Amurka.

Bisa al’adar Hausa, Mawaka sukan yi wa Mutane Waka, to amma a wani lokacin akan yi ma wakar mummunar fahimta, misali wakar da ya yi ta kusoshin Birni Uwawu da kuma wakar nan ta Na-malumfashi Habu Dan-mama, wanda masu fashin bakin wakoki su ke ganin cewa, wadannan wakoki ya yi sune domin ya nunawa Mutane cewar Yan zamani sun rasa inda za su kama, su basu kama Duniya ba kuma basu kama Lahira ba. To da aka tambayi Dr. Mamman Shata cewar shin ko wannan bayani na masu fashin bakin wakoki haka yake? sai ya ce“To wannan zance ne irin nasu , shi wanda naiwa ya san abinda na ce, kuma masu ji da basira sun san abinda na ce „

Daga cikin dalilan da suka sa Marigayi Dr. Mamman Shata ya ke yiwa Mutane Waka, akwai kwarewa akan sana’a misali wakar da ya yi ta Bawa Direba. An tambayi Marigayi Mamman Shata, shin waye Bawa direba dinnan? kuma mai ya sa ya yi masa waka? kuma da gaske ne dukkanin abubuwan da ya fada a cikin wannan waka ta Bawa Direba, gaskiya ne? haka abin yake, sai ya ce “Bawa jankin, shi kam Mutumin Katsina ne, amma a Musawa yai wayo, duk abinda na fadi a wakar Bawa haka yake ban kara masa ba, ban rage masa ba, kuma ko da ni ban fadi ba wani sai ya fadi „

Har ila yau Marigayi Dr Mamman Shata yakan yi wa manyan shugabanni waka, musamman ma wadanda suka tsayar da adalci, yanci, daidaito da kuma hadin kan al’umma. Misali wakar da ya yiwa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Allah ya jikan sa da rahama.

Sakamakon wakokin da marigayi Dr Mamman Shata ya yi domin amfanin Al’umma, ya samu yabo da jinjina da lambobin girmamawa. Misali a lokacin Mulkin Janar yakubu Gowon an ba shi lambar girma shi da marigayi Garba A.B.C.D. Kuma har ila yau Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bashi Digirin girmamawa na Dr. wanda sakamakon haka ya sa ake kiransa Dr. Mamman Shata Katsina. Haka kuma Mamman Shata ya dan fada cikin harkokin siyasa inda ma har aka zabeshi a matsayin kansila a wata mazaba a karamar hukumar Kankia da ke Jihar Katsina.[1]

Manazarta

gyara sashe

Shata: Oh, northerners stop sleeping, Our Nigeria, it's a pleasant place. Source: [1] Archived 2010-07-07 at the Wayback Machine