Jean-Marc Ithier
Jean-Marc Ithier (an haife shi a ranar 15 ga watan Yuli, shekara ta alif ɗari tara da sittin da biyar 1965 a Rodrigues) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Mauritius mai ritaya. Bayan Mauritius, ya taka leda a Afirka ta Kudu. [1]
Jean-Marc Ithier | |||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Rodrigues (en) , 15 ga Yuli, 1965 (59 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Moris | ||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka |
Sana'a
gyara sasheIthier ya koma kungiyar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu Engen Santos daga kungiyar Sunrise Flacq United ta Mauritius a shekara ta 1999, kuma ya buga wa kungiyar jama'a (people's team) wasa har zuwa lokacin da ya yi ritaya a shekara ta 2006. Yana da kusan kwallaye 70, kuma shi ne wanda ya fi kowa zura ƙwallo a raga a kulob ɗin.
An naɗa Ithier a matsayin kocin rikon kwarya na Engen Santos bayan tafiyar babban koci Roger De Sa wanda ya koma Bidvest Wits bayan kakar 06/07 amma daga baya David Bright na Botswana ya maye gurbinsa. Ithier ya zama mataimaki ga kocin kulob din na yanzu, Boebie Solomons. A cikin shekarar 2011, Ithier ya bar kulob din don shiga cikin aikinsa bayan ya yanke shawarar bude makarantar kwallon kafa wanda zai taimaka wajen bunkasa matasa masu fasaha.[2]
Ithier kuma a baya ya taba horar da 'yan wasan Afirka ta Kudu Homeless a gasar cin kofin duniya.[3]
Kididdigar sana'a
gyara sasheKwallayen kasa da kasa
gyara sashe# | Kwanan wata | Wuri | Abokin hamayya | Ci | Sakamako | Gasa | |||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
1. | 6 ga Yuni 1989 | Stade Linite, Victoria, Seychelles | </img> Seychelles | 2–1 | Nasara | Sada zumunci | |||||
2. | 24 ga Yuni 1990 | National Stadium, Gaborone, Botswana | </img> Botswana | 1-0 | Nasara | Sada zumunci | |||||
3. | 1 ga Yuli, 1990 | Independence Stadium, Windhoek, Namibia | </img> Namibiya | 2–1 | Nasara | Sada zumunci | |||||
4. | 25 ga Agusta, 1990 | Mahamasina Municipal Stadium, Antananarivo, Madagascar | </img> Seychelles | 2–0 | Nasara | 1990 Wasannin Tekun Indiya | |||||
5. | 27 ga Agusta, 1990 | Mahamasina Municipal Stadium, Antananarivo, Madagascar | </img> Comoros | 4–0 | Nasara | 1990 Wasannin Tekun Indiya | |||||
6. | 30 ga Agusta, 1990 | Mahamasina Municipal Stadium, Antananarivo, Madagascar | </img> Madagascar | 1-5 | Asara | 1990 Wasannin Tekun Indiya | |||||
7. | 9 ga Agusta, 1992 | Setsoto Stadium, Maseru, Lesotho | </img> Lesotho | 2–2 | Zana | Sada zumunci | |||||
8. | 25 ga Yuli, 1993 | Sir Anerood Jugnauth Stadium, Belle Vue Maurel, Mauritius | </img> Afirka ta Kudu | 1-3 | Asara | 1994 Gasar Cin Kofin Afirka Q. | |||||
9. | 23 ga Agusta, 1998 | Stade George V, Curepipe, Mauritius | </img> Lesotho | 3–1 | Nasara | 2000 Gasar Cin Kofin Afirka Q. | |||||
10. | 8 Oktoba 2000 | Stade George V, Curepipe, Mauritius | </img> Kongo | 1-2 | Asara | 2002 Gasar Cin Kofin Afirka Q. | |||||
11. | 6 Satumba 2003 | Stade George V, Curepipe, Mauritius | </img> Réunion | 2–1 | Nasara | 2003 Wasannin Tekun Indiya | |||||
Daidai kamar 17 Afrilu 2021 [4] |
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Ithier reveals how Pirates missed out" . kickoff.com.
- ↑ "Ithier Leaves" . Archived from the original on 2011-07-11. Retrieved 2011-07-12.
- ↑ "President Mbeki Welcomes Homeless World Cup" . Homeless World Cup. Archived from the original on 2008-12-16. Retrieved 2009-08-13.
- ↑ Jean-Marc Ithier - International Appearances - RSSSF