Akan yi wa ilimi kirari da cewa:

 • "Ilimi garkuwar Dan Adam."
 • "Ilimi Hasken rayuwa."
 • "Ilimi kogi ne"
Wikidata.svgsani
philosophical concept (en) Fassara da mental state (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na memory (en) Fassara
Karatun ta epistemology (en) Fassara
Has cause (en) Fassara koyo, qualia (en) Fassara da Wahayi
Contributing factor of (en) Fassara understanding (en) Fassara
Has quality (en) Fassara Knowledge environment (en) Fassara
Hannun riga da ignorance (en) Fassara
Amfani wajen knowledge management (en) Fassara
Tarihin maudu'i history of knowledge (en) Fassara
manhajar Koyar da yara

Ma'anar IlimiGyara

Ilimi

Ilimi shi ne: Sanin abu a bisa haƙiƙaninsa, sani na yanke shakka, na wani mutum ko wani abu, kamar su gaskiya ( kwatantaccen ilimi), iyawa (procedural knowledge), ko wasu abubuwa (acquaintance knowledge), mafi akasari bada gudunmuwar fahimta. Knowledge of facts, also referred to as propositional knowledge, is often defined as true belief that is distinct from opinion or guesswork by virtue of justification. Yayin da akwai yarda mai yawa tsakanin mafalsafa cewa wani irin yarda ce ta gaskiya, controɓersies da yawa suna maida hankali ne a falsafa wajen justification: ko ana ma buƙatarshi, yadda za'a fahimceshi, ko kuwa ana buƙatar wani abu bayan shi. Waɗannan controɓersies suna ƙara nauyaya ta dalilin wasu jerukan gwajin tunaninnuka na Edmund Gettier kuma ya taso da zaɓin ma'anoni dabam-dabam. Wasu suna ƙin cewa ana buƙatar justification kuma suna maye shi da, misali, reliability ko bayyanawar cognitive virtues. wasu suna jayayya cewa ana buƙatar justification amma suna formulating wasu requirements ɗin, misali, cewa babu defeaters babu kasancewar yarda ko kuma cewa mutumin ba zai samu yardar ba idan da ƙarya ce.

Shi ilmi wani irin baiwa ne da Allah Ya ke bayar wa ga bayin sa. Hakika, ilmi ya na tabbatuwa a cikin kwakwalwar dan adam. Mutum mai Ilmi ya sha banban da jahili ta kowacce fuska, saboda mai ilmi yana aiki ne ko barin aiki a sakamakon umarnin da ilmin sa zai ba shi, wato ai, ilmin zai kasance tamkar shi ne linzamin da ke jan ragamar hankalin sa da al’amuran sa.

lallai, ilmi fitila ne da ke haskaka Rayuwa. Duk mutumin da ba shi da ilmi, to hakika, za ka ga rayuwar sa cikin kunci ta ke.

Hanyoyin Samun IlimiGyara

Bincike.

Bincike hanya ce ta samu ilimi a wannan zamani da ba kamarta.

 • IYAYE

Hanya ta farko: Iyaye; Ana fara samun ilimin farko ne daga iyaye, musamman Mahaifiya. Daga gareta ne mutum yake fara koyar abubuwa iri-iri. Kamar su cin abinci, sanya tufafi, tarbiyyar rayuwa, tsafta da sauransu. Da taimakon mahaifi kuma yaro ya ke samun Juriya, Dogaro da Kai, Nagarta da kuma tabbatuwa a kan turba ta gari.

 • DANDALI.

Hanya ta biyu: Ita ce Dandali ko kuma mu ce rariya ko kan layi. Anan ne yaro yake koyon gane wadansu mutane daban da na gidan su. Kuma a nan ne yaro yake koyon wasanni da koyon zama da jama'a daban.

 • MAKARANTA.

Hanya ta uku: Makaranta; Daga hannun Iyaye kuma, sai makaranta. Anan mutum ya ke koyon ilimin Addini da Duniya. A Makarantar ne za a koyawa mutum ilimi daban-daban, tun daga Firamare zuwa Sakandire, har zuwa Jami'ah. A nan a ke samun shaidar karatu babba da karama don aiki a manya ko kananan ma'aikatu.

Nau'o'in IlimiGyara

Nau'o'in ilimi ya kasu ne zuwa gida uku kamar yarda masana suka tsara su.

 • ILIMIN ZAMANI (boko).
 • ILIMIN ADDINI.
 • ILIMIN GARGAJIYA.

Yanzu zamu dauko su daya bayan daya mudan tattauna akan su, amma a takaice.

Iimin Zamani (boko)Gyara

Shi ilimin zamani ko kuma muce boko kamar yarda akasarin hausawa muke kiran shi. Ya samo asaline daga Turawa wadanda suka yi mulkin mallaka a kasar mu Najeriya.

Turawan kasar Ingila su ne suka kawo mana ilimin boko a kasarmu ta Najeriya. Sun fara kaddamar da tsarin ilimin boko ne a sashen dukancin Najeriya kafin su gabatar da shi a yankin Arewacin Najeriya. Duk da dai lokacin turawa sun sha wahala harma da yake-yake kafin samun nasarar kaddamar da ilimin zamani a yankin Arewacin Najeriya amma kuma yanzu jama'ar yankin sun karbeshi hannu bibbiyu.

 • tsarin ilimin boko

Ilimin boko ilimine wanda yake da tsare tsare kafin, bayan da kuma lokacin da ake koyar da shi. Akwai tsare-tsare kafin a koyar da ilimin boko, kamar hukumomi daban-daban na ilimi su tsara abin da za'a koyar a shekara-shekara, zangunan karatu da kuma sati-sati, wanda ake kira da (SYLLABUS) a harshen Turanci. Sannan malami yana da tsare-tsaren da zai yi kafin shigar shi cikin aji wanda ake kira [LESSON PLAN] da kuma [LESSON NOTE] a turance.

Ilimin AddiniGyara

Ilimin addini, ilimine da ya samo asali bayan zuwan addinin Musulunci a Kasar Hausa .

 • tsarin Ilimin Addini.

Hanyar da ake bi wajen koyar da ilimin addini a gargajiya shine, idan yaro ya kai kamar shekara bakwai da haihuwa. Ana kaishi makarantar Alkur'ani wadda akafi sani da makarantar allo . Bayan yaro yayi saukar Kur'ani kuma, sai ya tafi makarantar da zai koyi karatun litattafai. Akasarin wannan karatun an fi yin sa ne a masallaci ko a gidan malamin da zai koyar.

Ilimin GargajiyaGyara

Ilimin gargajiya ilimi ne wanda ake koyon shi akasari a wajen da ake aiwatar da shi. Misali idan anaso yaro ya koyi yarda ake wata sana'a kamar kira , noma , kafinta kokuma jima to ana zaunar da shi ne a inda ake aiwatar da ita wannan sana'a din. A haka har ya koya kuma ya iya. To amma dayake yanzu zamani ya can kuma al'amurra da yawa sun sauya, duk sauran abubuwan da ake koyo a gargajiyance a yanzu an zamanantar dasu. Misali ana koyon noma, kafinta, saka a makaranta tun daga matakin firamare har yazuwa Jami'a.

 • domin karin bayani jeka