Amina Ibrahim Shekarau
Amina Ibrahim Shekarau ta kasance matar tsohon gwamnan jihar Kano,[1] Alhaji Ibrahim Shekarau kuma uwargida ga tsohuwar gwamnatin jihar Kano.[2][3][4]
Amina Ibrahim Shekarau | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 11 ga Yuni, 1968 (56 shekaru) |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Ibrahim Shekarau |
Sana'a |
Kuruciya da ilimi
gyara sasheAn haifi Amina Ibrahim a ranar 11 ga watan Yunin 1968 a Durumin Zungura Quarters, Kano.[3] Ta halarci Makarantar ta Old Kurmawa Primary School a tsakanin 1974 zuwa !980, sannan ta halarci fitacciyar Makarantar Sakandaren Mata ta Gwamnati, Jogana Kano tsakanin 1980 zuwa 1985. Ta shiga makarantar Midwifery Kano tsakanin 1985 zuwa 1989. A shekara ta 2001 da 2003, ta kasance daliba mai hazaka a Makarantar Nursing Kano.
Aiki
gyara sasheAmina ta kasance ma'aikaciya a tsawon wannan sana’ar tata. A tsakanin 1985 zuwa 1989 ta yi aiki a asibitin kwararru na Murtala Muhammad; tsakanin 1989 zuwa 1994 ya yi aiki a asibitin kwararru na Muhammadu Abdullahi Wase, Kano; A tsakanin shekarar 1994 zuwa 1998 ta yi aiki a asibitin yara na Hasiya Bayero, Kano.[3]
Kwarewa
gyara sasheAmina na da ilimi a fagen da ta kware kuma tana da ra'ayi a sauran fannuka kamar haka: Taron karawa juna sani kan inganta sabis na kula da marasa lafiya a cikin ƙarni (Nuwamba 2000), haɗin gwiwar mata kan HIV/AIDS (Agusta 2007); da kuma taron bita kan Protocol da tsaro (Agusta 2007).
Kyaututtuka da karramawa
gyara sashe- Jama'atu Ibadurrahman of Nigeria
- Mujahida Uwar Marayu ta Al-Ihsan Youth Movement
- Ambasada Ruwan Ruwa da Aikin Noma mai Dorewa ta wata kungiya mai zaman kanta (GWA) a Netherlands
- Shahadar karramawa ta Manarul Alhuda Islamiyya Islamic Women Center Fagge
- Takaddar Karramawa daga Kungiyar Tsofaffin Daliban Gama Tudu
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Ibrahim Shekarau biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2022-05-24.
- ↑ "Wives of LG chairmen in Kano tasked on water, sanitation". www.wofan-ng.org. Retrieved 2022-05-24.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 Kabir, Hajara Muhammad ([2010-]). Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657. Check date values in:
|date=
(help) - ↑ "Ramadan: Shekarau's Wife Supports Over 2,000 Vulnerable With Food Stuff – SolaceBase" (in Turanci). 2018-05-16. Retrieved 2022-05-24.[permanent dead link]