Herbert Eze
An naɗa Laftanar Kanal Herbert Obi-Eze, a matsayin shugaban mulkin soja a jihar Anambra dake Najeriya a cikin watan Agustan 1990 a lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida. A zamaninsa, Jihar Enugu ta rabu da Anambra a ranar 27 ga watan Agustan 1991, inda Obi-Eze ya ci gaba da zama gwamnan jihar Enugu. Ya miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan farar hula na jihar Enugu, Okwesilieze Nwodo a cikin watan Janairun 1992.[1]
Herbert Eze | |||||
---|---|---|---|---|---|
ga Augusta, 1990 - ga Janairu, 1992 ← Robert Akonobi (en) - Joseph Abulu →
ga Augusta, 1990 - ga Janairu, 1992 - Okwesilieze Nwodo → | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Herbert Obi-Eze | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Tarihin Mutanen Ibo | ||||
Harshen uwa | Harshen, Ibo | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa |
A cikin shekarar 2007 ya kasance shugaban kwamitin tsaro na jihar Imo.[2]