Henry Edmund Olufemi Adefope (An haife shi a ranar 15 ga watan Maris shekarar 1926 – Ya mutu a ranar 11 ga watan Maris shekara ta 2012) ya kasance babban Janar din Sojan Najeriya wanda ya rike mukamin Ministan Harkokin Kasashen Waje kuma ya zama memba na Kwamitin Gasar Olympics na Duniya daga. Shekarar 1985 zuwa shekara ta 2006 kuma memba mai girmamawa na Kwamitin Gasar ta Duniya tun shekara ta 2007[1]

Henry Adefope
Ministan harkan kasan waje Najeriya

ga Augusta, 1978 - Satumba 1979
Joseph Nanven Garba - Ishaya Audu
Nigerian Minister of Labour (en) Fassara

1975 - 1978
mataimakin shugaba

1974 - 1982
president (en) Fassara

1967 - 1976
Rayuwa
Haihuwa Jahar Kaduna, 15 ga Maris, 1926
ƙasa Najeriya
Ƙabila Yaren Yarbawa
Harshen uwa Yarbanci
Mutuwa Lagos,, 11 ga Maris, 2012
Karatu
Makaranta University of Glasgow (en) Fassara
Makarantar Nahawu ta CMS, Lagos
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya, ɗan siyasa, soja da likita
Kyaututtuka
Mamba International Olympic Committee (en) Fassara
Rundunonin, Sojin Najeriya
Digiri major general of tank forces (en) Fassara
Henry Adefope a kwamitin wasannin Olympics na duniya

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Henry Adefope a ranar 15 ga watan Maris shekara ta 1926 a Kaduna, Nigeria da Alice Adefope da Cif Adefope. Yayi karatun sa a CMS Grammar School, Lagos da Glasgow University, ya kuma kammala karatun sa a General medicine a shekarar 1952. Ya yi aiki a matsayin likita daga shekarar 1953 zuwa shekara ta 1963 sannan aka ba shi aikin soja a shekara ta 1963.

Ya hau mukamin Manjo Janar kuma ya yi aiki a matsayin Daraktan kula da lafiya. Daga shekarar 1975 zuwa shekara ta 1978 ya zama Ministan kwadago sannan daga shekara ta 1978 zuwa shekarar 1979 ya zama Ministan Harkokin Kasashen Waje, dukkanin mukaman ministocin karkashin gwamnatin soja ta Janar Olusegun Obasanjo .

Adefope ya kuma yi aiki a mukamai daban-daban a harkokin gudanar da wasanni, ciki har da shugabanci na Shugaban Kwamitin Wasannin Olympics na Najeriya daga shekarar 1967 zuwa shekara ta 1976 da kuma Mataimakin Shugaban Kungiyar Wasannin Kasashe ta Tsakiya daga shekarar 1974 zuwa shekara ta 1982. A shekarar 1985 aka zaɓe shi a cikin IOC. Yayin da yake tare da IOC, ya kasance memba na kwamitocin da suka zaɓi biranen da za su karɓi bakuncin gasar wasannin Olympics ta bazara ta shekarar 2000 da shekara ta 2004 . An bincika shi, amma an barrantar da shi game da badakalar neman gasar Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2002 . [2] Ya zama memba na girmamawa na IOC a shekara ta 2006.

Adefope ya kasance uba, kaka da kakana. ‘Ya’yan sa sun hada da Femi Adefope, Dotun Okojie, Folake Nedd, Ronke Eso, Seyi Adefope, Niyi Adefope da Toyin Adeyeye.[3]

Henry Adefope ya mutu a ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2012 yana da shekara 85, kwana hudu ke nan da cikarsa shekaru 86 da haihuwa.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Former Nigerian IOC member, Adefope, dies at 86". Afriquejet.com. Archived from the original on 2012-07-30. Retrieved 2012-03-13.
  2. "Commission Recommends Censure to IOC Members". Archived from the original on 2012-11-04. Retrieved 2020-11-20.
  3. Admin. "Veterans mourn General Adefope (Rtd)". Vanguard. Retrieved 25 January 2019.

Hanyoyin haɗin waje

gyara sashe
Political offices
Magabata
Joseph Nanven Garba
Foreign Minister of Nigeria
1978 – 1979
Magaji
Ishaya Audu