Harin bom a Maiduguri, Yuli 2014

Harin bom a Najeriya

A ranar 1 ga watan Yulin 2014, wata motar dakon kaya ɗauke da gawayi da bama-bamai ta fashe a Maiduguri, jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.[1][2] An tayar da bam ɗinne da misalin karfe 8 na safe a wata unguwa da ke kusa da wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a, inda ya kashe aƙalla mutane 56 tare da lalata motoci da dama.[1][2]

Infotaula d'esdevenimentHarin bom a Maiduguri, Yuli 2014
Iri bomb attack (en) Fassara
Kwanan watan 1 ga Yuli, 2014
Wuri Maiduguri
Adadin waɗanda suka rasu 56

Boko Haram

gyara sashe

Jami'an tsaro sun yi imanin cewa waɗanda suka aikata wannan aika-aika ƴan ƙungiyar Boko Haram ne, kungiyar ta'addanci da tada kayar baya ta faro tun a shekarar 2009.[1][2] Boko Haram sun fi kai hari Maiduguri fiye da kowane matsuguni.[2] Wadannan hare-haren sun haɗa da na Yuli 2009, Disamba 2010, Mayu 2011, Nuwamba 2011, Janairu 2012, Disamba 2012, Janairu 2014, Nuwamba 2014, Janairu 2015, Maris 2015, Maris 2015, Satumba 2015, Maris 2015, Maris 2015, Maris 2015

Manazarta

gyara sashe