Rikicin a Arewacin Najeriya, Disamba 2012
Rikincin harbe-harbe guda biyu a Najeriya ya faru ne ranar bikin Kirsimeti a arewacin Najeriya, a ranar 25 ga watan Disamba, 2012, a cikin wasu coci-coci da ke Maiduguri da Potiskum. Aƙalla mutane goma sha biyu ne suka jikkata. Ƙungiyar Boko Haram ta yi iƙirarin cewa ba ta da alhakin kai harin, amman kuma “biri yai kama da mutum”-(ana zargin ƙungiyar ita ta kai harin).[1]
Rikicin a Arewacin Najeriya, Disamba 2012 | ||||
---|---|---|---|---|
mass shooting (en) | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya | |||
Kasancewa a yanki na lokaci | UTC+01:00 | |||
Kwanan wata | 28 Disamba 2012 | |||
Wuri | ||||
|
Lamarin
gyara sasheA Potiskum
gyara sasheA garin Potiskum na jihar Yobe da ke arewa maso gabashin ƙasar, wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun harbe kimanin mutane 6 masu tafiya zuwa coci. Bayan haka an banka wa cocin wuta.
A Maiduguri
gyara sasheA Maiduguri kuma an kashe wasu suma, masu niyyar zuwa coci su 6 ciki har da limamin cocin.[2]
Bayan nan
gyara sasheBayan kwana uku, a ranar 28 ga Disamba, a ƙauyen Musari, an kashe wasu Kiristoci goma sha biyar. Maharan sun mamaye ƙauyen inda sukai musu yankan rago a yayin da suke tsaka da barci. Wadanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da jami’in ƴan sandan hanya da fararen hula goma sha huɗu.[3]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Deadly Christmas attack on Nigeria church – Africa". Al Jazeera English. December 25, 2012. Retrieved December 25, 2012.
- ↑ "12 killed in attacks on two churches in Nigeria". CNN. December 25, 2012. Retrieved December 25, 2012.
- ↑ "Vijftien christenen gedood in dorp Musari – Het Nieuwsblad" [Fifteen Christians slain in Muscari village]. Nieuwsblad.be (in Holanci). December 30, 2012. Retrieved January 5, 2013.