Harin Bom a Maiduguri, Maris 2017
Harin ƙuna baƙin wake a Najeriya
A ranar 22 ga watan Maris 2017, da misalin karfe 4:30 na safe, wasu bama-bamai sun tashi a wurare uku a unguwar Muna Garage da ke Maiduguri, jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya.[1][2]
Harin Bom a Maiduguri, 2017 | ||||
---|---|---|---|---|
suicide bombing (en) | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya | |||
Kwanan wata | 22 ga Maris, 2017 | |||
Wuri | ||||
|
Harin
gyara sasheFashe-fashen sun faru ne a sansanin ' yan gudun hijira na Garage Muna.[3]
Hare-haren da ƴan ƙuna baƙin wake uku zuwa biyar suka kai a wurare daban-daban, sun yi sanadiyar mutuwar mazauna sansanin farar hula uku zuwa biyar da kuma su kansu (ƴan ƙuna baƙin wake)- tare da jikkata mutane 20.[1][3]
Iƙirari
gyara sasheBabu wata ƙungiyar ta'addanci da ta yi iƙirarin ko ta ɗauki nauyin alhakin wadannan fashe- fashe, amma ana kyautata zaton ƙungiyar Boko Haram mai jihadi - wacce ta kai hari a Maiduguri sau da yawa a baya - ita ce ke da alhakin kai harin.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Suicide bomber kills 10 in northeastern Nigeria market". thisdaylive.com. Archived from the original on 2017-03-24. Retrieved 2017-03-23.
- ↑ CNBC (2017-03-22). "Blasts kill 4, injure 18 in northeastern Nigeria, police say". CNBC. Retrieved 2017-03-23.
- ↑ 3.0 3.1 Ahovi, Isa Abdulsalami (23 March 2017). "Five suspected bombers, three IDPs die in Borno multiple blasts" (in Turanci). Archived from the original on 2017-03-23. Retrieved 2017-03-23.
- ↑ "Multiple bomb blasts rock Nigeria's Maiduguri". aljazeera.com. Archived from the original on 2020-09-04. Retrieved 2022-12-28.