Hari a Maiduguri, Maris 2015
A ranar 7 ga watan Maris, 2015 wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a kan keken sa a kusa da kasuwar kifi dake Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya, inda ya kashe aƙalla mutane 10.[1][2][3] Bayan haka kuma a hukumance an bayar da rahoton cewa, an kai wasu jerin hare-haren ƙwara biyar da ƴan ƙunar baƙin wake suka kai a rana guda a yankuna biyar na birnin. A cewar majiyoyi da yawa, an kashe mutane 58 sannan, sama da mutane 143 suka jikkata.[4][2][5]
Hari a Maiduguri, Maris 2015 | ||||
---|---|---|---|---|
suicide bombing (en) | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya | |||
Kwanan wata | 7 ga Maris, 2015 | |||
Wuri | ||||
|
Lamarin
gyara sasheKamar yadda shaidu da rahotanni daban-daban suka bayyana, mai yiwuwa dan ƙuna baƙin wake na farko yaro ne ɗan shekara 16[6] wanda ya yi ƙoƙarin shiga kasuwar kifi ta Baga a birnin Maiduguri.[6]
Ana kyautata zaton fashewar ta biyu ce, ta tashi a wata kasuwa da aka fi sani da kasuwar litinin da misalin karfe 12:30. Rahotanni daga BBC sun ce wasu mata biyu ne suka kai harin.[6] Fashewa na uku ya faru ne da misalin karfe 12:52 kusa da ofishin tsaro na ma'aikatar harkokin wajen ƙasar. A cewar rahoton na BBC, "Shaidu da yawa sun yi imanin cewa fashewar tagwaye ce kuma". [6]
Alhaki
gyara sasheBabu wata ƙungiyar ta’addanci da ta ɗauki alhakin wadannan fashe-fashen nan take, amma majiyoyi da dama sun yi nuni da cewa ƙungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram ce ke da alhakin kai harin[7][8] domin fashe-fashen na da kamanceceniya da irin hare-haren Boko Haram a baya.[9]
A ranar 8 ga watan Maris, 2015 adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 58, a cewar ƴan sandan Najeriya.[10]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Suicide bomber kills 10 in northeastern Nigeria market". timesofindia.com. Archived from the original on 2015-04-04. Retrieved 2023-01-06.
- ↑ 2.0 2.1 "BBC News - Nigerian city of Maiduguri hit by multiple blasts". BBC News.
- ↑ "5 suicide blasts hit Nigerian city of Maiduguri, 54 killed". Yahoo News. 7 March 2015.
- ↑ ABC News. "5 Suicide Bomb Blasts Rock Maiduguri City in Northeast Nigeria, 54 Dead, 143 Wounded: Official". ABC News. Retrieved 8 March 2015.
- ↑ "Maiduguri Multiple Bomb Attacks: 55 killed, 146 injured in five suicide attacks - Premium Times Nigeria". Premium Times Nigeria. Retrieved 25 September 2015.
- ↑ 6.0 6.1 6.2 6.3 Akinshilo Ayomide. "Multiple Bomb Attacks Claim 58 Lives In Maiduguri". NEWS.NAIJ.COM - Nigerian & worldwide news. Retrieved 8 March 2015.
- ↑ "Four 'Boko Haram' suicide bomb attacks kills 54, wounds 143 in northeast Nigeria". International Business Times UK. Retrieved 8 March 2015.
- ↑ "Suspected Boko Haram suicide blasts in Nigerian city kill at least 54". Fox News. Retrieved 8 March 2015.
- ↑ "Suicide bomb attacks kill dozens in Nigerian city of Maiduguri". the Guardian. Retrieved 8 March 2015.
- ↑ Drew Hinshaw and Gbenga Akingbule (8 March 2015). "Death Toll Increases in Nigeria Suicide Bombings". WSJ. Retrieved 25 September 2015.