Harin bam a Maiduguri, Maris 2016

Harin yan ta'adda a masallaci a Maiduguri, Najeriya

A ranar 16 ga watan Maris 2016, wasu mata biyu ƴan ƙuna baƙin wake, waɗanda ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne, sun kashe mutane 22 da suke ibada a masallacin Molai-Umarari da ke wajen birnin Maiduguri, Najeriya. Bam na farko ya tashi ne da misalin karfe 5 na safe a daidai lokacin da masu ibada ke fara sallar asuba.[1][2]

Harin bam a Maiduguri, 2016
suicide bombing (en) Fassara
Bayanai
Bangare na Rikicin Boko Haram
Ƙasa Najeriya
Kwanan wata 16 ga Maris, 2016
Wuri
Map
 11°50′N 13°09′E / 11.83°N 13.15°E / 11.83; 13.15
tambarin Boko Haram

Ɗaya daga cikin matan ta yi kama da namiji don ba ta damar shiga wuraren masallacin da mata ba sa iya shiga.[3][4] Ta tsaya a layin gaba na masallacin, sannan ta tayar da bama-baman da ke jikinta a lokacin da mutane ke mikewa domin fara sallah.[5]

Bayan da aka tayar da bam na farko a cikin ginin, na biyun kuma ya tashi nisan mita 50 metres (160 ft) daga wajen masallacin, inda ya kashe mutanen da suke yunƙurin tserewa daga ginin, da kuma waɗanda suka zo domin bada agajin gaggawa.[6][2]

Hare-haren sun zo ne jim kaɗan bayan shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi ikirarin cewa "an karya lagon ƴan Boko Haram". Bayan haka, don kare waɗannan ikirari, jami'an soji sun yi watsi da tsananin lamarin a matsayin wani abu na yau da kullun, wanda 'kasashe na duniya' suka fuskanta.[7]

Maiduguri

gyara sashe

Maiduguri ita ce mahaifar reshen ƙungiyar Boko Haram da ke ɗauke da makamai. Masallacin yana cikin Umarari, ƙauye 4 miles (6.4 km) daga birnin, wanda aka mayar da shi cibiyar bayar da umarni ga rundunar sojin Najeriya da ke yaki da ƙungiyar.[6] An kai wani hari kusan makamancin haka watanni biyar da suka gabata, inda babban limamin masallacin ya tsira. An sake buɗe masallacin ne kwanaki uku kacal kafin aukuwar lamarin.[8]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. "Nigeria mosque hit by Maiduguri suicide bombers". BBC News.
  2. 2.0 2.1 Ndahi Marama, Levinus Nwabughiogu (17 March 2016). "How Twin Suicide Bombers Killed 22 Worshippers At Borno Mosque". Vanguard. Lagos. Missing or empty |url= (help)
  3. "2 Female Suicide Bombers Attack Mosque Near Maiduguri, Nigeria, Killing Over 20". The New York Times. 17 March 2016.
  4. Ola, Lanre (16 March 2016). "Two Suicide Bombers Kill 22 at Mosque in Northeast Nigeria's Maiduguri". Reuters.
  5. "Two suicide bombers kill 22 in Maiduguri, NE Nigeria". Agence France Presse. 16 March 2016. Missing or empty |url= (help)
  6. 6.0 6.1 "Nigeria mosque bombers kill 22". Al Jazeera.
  7. Iaccino, Ludovica (16 March 2016). "ConflictNigeria Boko Haram ISIS Maiduguri bombers: Boko Haram-style attacks also happen in Europe, says Nigerian ministry". International Business Times. Retrieved 24 March 2016.
  8. Alfa, Ismail; Omirin, Joshua (16 March 2016). "Rescuers: Female suicide bombers kill 24 at Nigerian mosque". Associated Press. Retrieved 17 September 2021.