Hari a Jihar Borno, Satumba 2015
A yammacin ranar 20 ga watan Satumba, 2015, an kai jerin hare-haren bama-bamai a Maiduguri da Monguno, a Najeriya, inda aka kashe akalla mutane 145. da kuma raunata akalla wasu su 97. Mafi yawan wadanda suka jikkata harin ya rutsa dasu ne a Maiduguri inda wasu ababen farfashewa ƙwara huɗu suka halaka aƙalla mutane 117 .
| ||||
Iri | harin ta'addanci | |||
---|---|---|---|---|
Kwanan watan | 20 Satumba 2015 | |||
Wuri |
Maiduguri Monguno | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Adadin waɗanda suka rasu | 117 |
Hari
gyara sasheHare-haren bama-baman sun faru ne bayan fiye da wata guda ba tare da samun wata matsala ba a birnin Maiduguri daga ƙungiyar tada ƙayar bayanan da dai ƙaurin suna, wato Boko Haram mai tsattsauran ra'ayi.[1] Wani farmaki da sojojin Najeriya suka kai a watan Agusta, inda suka fatattaki ƴan Boko Haram daga sansanonin su a yankin, ya haifar da raguwar hare-hare.[1][2] Tun da farko ranar 20 ga watan Satumba; shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da wani faifan bidiyo yana ƙaryata ikirarin da sojojin Najeriya suka yi na cewa an fatattaki Boko Haram.[3][4] Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai hare-haren, kodayake ana zargin ƙungiyar Boko Haram.[5] Kakakin rundunar sojin Najeriya Sani Usman ya bayyana cewa, taron ya nuna irin halin da 'yan Boko Haram ke ciki.[5] Abba Mohammed Bashir Shuwa, hadimin gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana cewa maharan sun yi amfani da damar da jama'a suka taru domin bukukuwan karamar Sallah.[6]
A Maiduguri
gyara sasheMisalin karfe 7:30;lokacin gida (18:30;UTC ) na ranar 20 ga watan Satumba; [7] An tayar da wasu bama-bamai guda huɗu a faɗin Maiduguri, babban birni a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, a cikin shekaru 20, inda suka kashe aƙalla mutane 54..[5][8][9] Waɗannan ne hare-hare mafi girma da aka kai a birnin tun cikin watan Maris;7, 2015, lokacin da wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da ake dangantawa da Boko Haram suka kashe mutane 58.[10][11]
Wani ɗan ƙuna baƙin wake ya tayar da bama -bamai, samfurin-(IED) a wani masallaci da ke Ajilari,[1] ya kashe akalla mutane 43.[9] Fashewar ta biyu (ta bom ɗin) ta faru a wata kasuwa da ke birnin bayan da ƴan ta’addar suka jefa bama-bamai a cikin wata cibiyar kallo (gidan kallon fina-fina, ko cinima), inda suka kashe aƙalla mutane 11[1][9] ko aƙalla su 15 da suka rasa rayukansu.[12] Harin bam na huɗu ya faru ne a wata cibiyar wasanni (shagunan buga games na TV. Misali wasan kamfuta na Playsatatio).[3] Mai magana da yawun ƴan sanda; Victor Isuku, ya bayyana cewa aƙalla mutane 97 ne suka jikkata.[8] Wata ƙungiyar kare fararen hula ta bayar da rahoton cewa aƙalla mutane 80; aka kashe, mutane a cikin birnin kuma sun bayyana cewa ƴan sanda sun bayar da rahoton raguwar adaɗin saboda iyalai da ke binne mamatansu nan da nan.[13] Mazauna yankin sun ce adaɗin ya zarta haka, ciki har da akalla 85 da suka mutu.[12] A ranar 22, ga watan Satumba; asibitocin gida sun ba da rahoton cewa aƙalla mutane 117 an sanar da mutuwar su, daga cikin su, su 72 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da kuma 45 a asibitin kwararru na jihar Borno.[14]
A Monguno
gyara sasheKimanin sa'o'i biyu bayan tashin bama-bamai a Maiduguri, an sake tayar da wasu bama-bamai biyu a wani shingen bincike a cikin kasuwar Monguno kimanin kilomita 135 daga birnin Maiduguri. Ya kashe akalla mutane 28.[7][8]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 Lanre Ola & Julia Payne (September 21, 2015). "At least 54 people killed in bomb blasts in Nigeria's Maiduguri". Maiduguri, Nigeria: Reuters. Retrieved September 21, 2015.
- ↑ "DHQ: Nigerian Troops Have Destroyed All Boko Haram Camps". This Day Live. 10 September 2015. Archived from the original on 13 September 2015. Retrieved 10 September 2015.
- ↑ 3.0 3.1 "50 killed in multiple blasts in Nigeria". Business Standard. September 21, 2015. Retrieved September 21, 2015.
- ↑ Ludovica Iaccino (September 21, 2015). "Boko Haram leader Abubakar Shekau calls Nigerian Army liars as deadly attacks continue". International Business Times. Retrieved September 21, 2015.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 "Nigeria's Boko Haram crisis: Maiduguri blasts kill dozens". BBC News. September 21, 2015. Retrieved September 21, 2015.
- ↑ Norimitsu Onishi (September 22, 2015). "More than 100 Killed by Boko Haram Bombings in Nigeria". New York Times. Abuja, Nigeria. Retrieved September 22, 2015.
- ↑ 7.0 7.1 Lanre Ola; Isaac Abrak; Alexis Akwagyiram & Julia Payne (September 22, 2015). "At least 80 people killed in bomb blasts in Nigeria's Borno state". Maiduguri, Nigeria: Reuters. Archived from the original on September 23, 2015. Retrieved September 22, 2015.
- ↑ 8.0 8.1 8.2 "Extremist attack killed at least 100 in Nigeria, defense group says". Maiduguri, Nigeria: CBS News. Associated Press. September 22, 2015. Retrieved September 22, 2015.
- ↑ 9.0 9.1 9.2 "Dozens die in blasts in Borno state capital, Nigerian official says". Abuja, Nigeria: CBS News. Associated Press. September 22, 2015. Retrieved September 22, 2015.
- ↑ "Nigerian city of Maiduguri hit by multiple blasts". BBC News. September 21, 2015. Retrieved September 22, 2015.
- ↑ "5 suicide blasts hit Nigerian city of Maiduguri, 54 killed". Yahoo News. 7 March 2015.
- ↑ 12.0 12.1 Bukar Hussain (September 21, 2015). "85 dead in new Boko Haram strike on Nigeria's Maiduguri". Yahoo! News. Agence France-Pressse. Archived from the original on September 23, 2015. Retrieved September 21, 2015.
- ↑ Jossy Ola (September 22, 2015). "Nigeria defense group: At least 100 killed in Sunday's blasts in northeastern Borno state". U.S. News. Associated Press. Retrieved September 22, 2015.
- ↑ "Death toll hits 117 after NE Nigeria bombings: medics". Maiduguri, Nigeria: Yahoo! News. Agence France-Presse. September 22, 2015. Archived from the original on September 23, 2015. Retrieved September 22, 2015.