Mallam Garba Shehu (an haifeshi ranar 27 ga watan Nuwamba shekara ta alif dari tara da hamsin da tara miladiyya 1959) ɗan Jarida ne kuma ɗan siyasa ne wanda ya kasance a matsayin Babban Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai ga tsohon Shugaban Tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari. [1] Ya kasance shugaban ƙungiyar Editocin Najeriya kuma yayi magana game da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar.

Garba Shehu
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

3 ga Yuni, 2003 -
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Bayanan Fage gyara sashe

An haife shi a garin Dutse, jihar Jigawa. Kuma ya taso ne tare da iyayensa duk a jihar ta Jigawa.

Ilimi gyara sashe

Shehu ya halarci makarantar firamare ta Dutse a shekarar alif ɗari tara da saba'in, 1970. Daga nan ya wuce Kwalejin Barewa, Zariya a shekara ta alif ɗari tara da saba'in da biyar, 1975. Acikin shekara ta alif ɗari tara da da tamanin da ɗaya, 1981, ya sami Digiri na farko a Jami’ar Bayero. Kano.

Ayyuka gyara sashe

Shehu ya fara aikin sa ne a matsayin wakili a Gidan Talabijin na Najeriya, Sakkwato acikin shekara ta 1982. Sannan ya kasance wakilin labarai na makamashi a Network News Lagos a cikin shekara ta 1984. Ya yi aiki a matsayin Shugaban Editocin Guild na Najeriya, shi ne darekta a lokacin Media da Publicity na Dukkanin 'yan majalissun ci gaban yakin neman zaben shugaban kasa acikin shekara ta 2015. Acikin shekarar 2015, shugaban tarayyar Najeriya Muhammad Buhari, ya nada shi a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai kuma yanzu haka yana rubutu a matsayin jaridar Premium Times ta Najeriya.

Manazarta gyara sashe