Durbar

anayinsa a yankuna daban daban a najeriya

Hawan Durbar ko Bikin Durbar wani tsohon bikin al'adane wanda yake gudana shekara-shekara a wasu daga cikin jahohin Najeriya. Wannan bikin na nuna murnan zuwan karshen watan Ramadana da kuma gabatar da bikin karamar Sallah da babbar Sallah.[1][2]

Infotaula d'esdevenimentDurbar

Iri biki
Validity (en) Fassara 1911 –
Wuri Jihar Borno, jihar Kano, Jihar Katsina, jihar Sokoto, Lafia, Jihar Gombe, Jihar Bauchi da Masarautar Akko
Ƙasa Najeriya
Mahayin doki a bikin Durbar a birnin Kano shekarar 2006
Bikin Dutbar a Birnin Bidda na jahar Neja a Arewacin Najeriya

Ana fara gabatar da bikin Durbar ne da sallar Idi a safiyar ranan sannan kuma sai sarki ya fito tare da mahaya dawaki da mawaka da 'yan takiya su fito a jere a fara sukuwa da dawakai. Sannan sai wazirai da hakimai da sauran 'yan fada su fito suna miqa gisuwa ga sarki suna mai mika wuya ga masarautarsu.

Asalin bikin Durbar ya fara ne a karni na 14 a Kano babban birnin arewacin Najeriya. Anfi sanin bikin ne a manayan biranen hausa kamar Kano, Sakkwato, Zariya, Katsina da Bida kuma yana jawo hankulan yan yawon bude ido.[3][4]


Tarihin Durbar

gyara sashe
 
Yara a Katsina suna yin wasan Daba. (yara na kamanta irin wannan hawa na daba inda suke samar da sarki da dogarai daga cikinsu sannan kuma sunayin amfani da karare wajen yin dokin wasa na kara. Irin wannan yana faruwa a birane da wasu garuruwa a kasar Hausa
 
Durbar a Bauchi
 
Durbar a Zaria
 
Durbar a Kano

Turawan mulkin mallaka ne suka kawo bikin Durbar a Najeriya. Amma asalin kalmar Durbar tazo ne daga harshen Farisa daga bukuwan nuna goyon baya ga saraunia Biktoriya amatsayin Sarauniyar Indiya bayan shigar turawan mulkin mallaka na Birtanya kasar ta Indiya a shekarar 1877. An fara bikin durbar na farko ne a Najeriya cikin shekarar 1911, daga baya bikin yaci gaba ashekarun 1924, 1925, 1948, 1960 da 1972. Bikin yaci gaba a kasar har ya zuwa yanzu kuma yana daga cikin muhimman bukukuwa a Arewacin Najeriya.

Bayan samun 'yanci

gyara sashe

An gabatar da bikin Durbar a taron 2nd World Black and African Festival of Arts and Culture wanda akafi sani bikin FESTAC 77. A hankali turawa suka cusa son bikin na durbar domin su karama sojoji kaimi wajen hawan dokuna tare da kara kawata Bikin Sallah.

Manazarta

gyara sashe
  1. "A 100-Year-Old Muslim Festival of Horse Riding". Folio Nigeria. Retrieved 17 August 2020.
  2. "In Kano, a thrilling display of ancient Durbar festival marks Eid el Fitr | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2016-07-08. Retrieved 2021-08-25.
  3. "Kano Durbar Festival: Nigeria's Most Spectacular Horseparade". Google Arts & Culture (in Turanci). Retrieved 2021-08-02.
  4. "Kano Durbar Festival: Nigeria's Most Spectacular Horseparade". Google Arts & Culture (in Turanci). Retrieved 2021-08-25.