Arewa 24
AREWA24 Tashar talabijin ce ta tauraron dan adam a Najeriya wacce ake samu a DSTV, GOtv, Startimes, da canal+ wanda ke nuna salon rayuwar Yankin Arewacin Najeriya. Tashar tana daga cikin tashoshi na farko na harshen hausa. Tashar talabijin ta Arewa 24 tana yaɗa shirye-shiryenta ga masu kallo sama da mutum miliyan 40 a Najeriya da Yammacin Afirka, a cewar tashar wadda ke bikin shekara bakwai da kafuwa. Tashar wadda ke da babban ofishi a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, a ranar Litinin 28 ga watan Yunin 2022, ta cika shekara takwas cur da kafuwa.
Arewa 24 | |
---|---|
| |
Bayanai | |
Iri | tashar talabijin |
Ƙasa | Najeriya |
Aiki | |
Bangare na | sherin television a najeriya |
arewa24.com |
Arewa 24 tasha ce da ke yana shirye-shiryen da suka shafi rayuwar Hausawa ta yau da kullum cikin harshen Hausa - tsakanin kafofi irinsu BBC Hausa da ke yana labarai kawai. Wata sanarwa daga tashar ta ce an kafa ta ne "domin cike wagegen gini" a arewacin Najeriya.(Ihayatu (talk) 22:20, 30 Mayu 2023 (UTC)).[1](Ihayatu (talk) 22:20, 30 Mayu 2023 (UTC))
Tarihi.
gyara sasheAREWA24 mallakar Equal Access ce kuma tana daukar nauyin shirye-shiryen al'adu da ilimantarwa ga mutanen arewacin Najeriya a cikin harshen hausa. Cibiyar sadarwar tashar ita ce Nilesat. An kirkiro AREWA24 ne a shekara ta 2013, domin cike gurbi a cikin shirye shiryen nishadi da kuma salon rayuwa na harshen hausa. Kaddamarwar ta ci kusan dala miliyan bakwai kuma Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ce ta dauki nauyinta. Tashar ita ce tashar talabijin ta farko da ake gabatar da shirye-shiryenta 24/7 da harshen Hausa wacce ta samo asali daga gina zaman lafiya da nishadi. A cewar shafin yanar gizon Equal Access International, tashar na nufin fadada al'adun Arewacin Najeriya, tare da samar da alfahari da al'adu. A shekara ta 2017, AREWA24 ta yi aiki tare da Eutelsat Communication don bunkasa damarta a matsayin tashar talabijin ta kyauta a yankin Kudu da Saharar Afirka don masu jin Hausa. A shekara ta 2018, tashar ta kara waka da wasanni a cikin harshen hausa. A wannan shekarar, AREWA24 ta kulla sabuwar kawance da kungiyar Girl Effect don tallafawa nasarar 'yan mata a arewacin Najeriya. Tashar ta kuma hada hannu da finafinan Kannywood da ke Kano, Najeriya.[2]
Bikin Cikar Arewa24 Shekara 7 da Kafuwa.
gyara sasheTashar talabijin ta Arewa 24 tana yana shirye-shiryenta ga masu kallo miliyan 40 a Najeriya da Yammacin Afirka, a cewar tashar wadda ke bikin shekara bakwai da kafuwa. Tashar wadda ke da babban ofishi a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, a yau Litinin 28 ga watan Yunin 2021, ta cika shekara bakwai cur da kafuwa. Arewa 24 tasha ce da ke yana shirye-shiryen da suka shafi rayuwar Hausawa ta yau da kullum cikin harshen Hausa – saɓanin kafofi irinsu BBC Hausa da ke yana labarai kawai. Wata sanarwa daga tashar ta ce an kafa ta ne “domin cike wagegen giɓi” a arewacin Najeriya. “An kafa tashar Arewa 24 a shekarar 2014, domin cike wawakeken ginin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishaɗi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya da al’adu da kaɗe-kare da fina-finai da fasaha da girke-girke da kuma wasanni.” Shugaban Arewa 24, Jacob Arback ya ce: “Mutane da dama ba su fahimci cewa akwai mutane masu magana da harshen Hausa sama da milyan 80 a Arewacin Najeriya da kuma yankin Sahel ba, kuma yankin na cike da matasa masu basira a ko’ina. “Sai dai abin da na fi alfahari da shi, shi ne yadda hukumar gudanarwa da ma’aikatanmu suka tattaru daga bangarori na rayuwa daban-daban da addinai da ƙabilu da kuma yankunan Najeriya daban-daban.” Tashar na da ɗumbin mabiya a shafukan sada zumunta da suka haɗa da Facebook (1,397,067) da Twitter (124.5K) da Instagram (1.7k). [3]
SHIRYEN-SHIRYEN DA SUKE WAKANA A YANZU.
gyara sashe- Gari ya waye
- Dadin Kowa
- Kwana Casa'in
- Fina-finan Kannywood
- H Hip Hop
- Zafafa 10
- Akushi Da Rufi
- Ubongo Kids
- Akili & Me
- Mata A Yau
- Kaddarar Rayuwa
- Lafiya Jari
- Labarina (Shiri Mai dogon zongo)
- Waiwaye
- Rayuwar matasa
- Dandalin taurari
- Ado da kwalliya
- Rahotanni
- Shahararrun wakoki
- Al'adun mu
- Gidan badamasi
- Manyan mata
- Zamantakewa
- Mai ake yayi
- zabin Raina
- Tarkon kauna
- Gidan sarauta
- Nunu da andalu
- Mata a yau
- Daga titi
- A wanan rana.
Shirin Gari ya waye.
gyara sasheShirin GARI YA WAYE, shiri ne na musamman na Gidan AREWA24 da ke kawo muku a kowacce safiya, shirin yana duba ne ga dukkanin rayuwar Arewacin Najeriya; Al’adu da Wasanni da Matasa da al’amuran dake faruwa yau da gobe na Fasaha da Wasannin Kwaikwayo da Kiwon Lafiya da Motsa Jiki, Zamantakewa, Harkokin Kasuwanci, Nishadantarwa da Jaruman ‘Yanwasa da ma wasun su, Shirye-shiryen Gari ya waye sun hada da Tattaunawa akan muhimman batutuwa da Rahotanni da suka saba zuwa a cikin shirin.[4]
Shirin Akushi da rufi.
gyara sasheShirin Akushi Da Rufi wanda Kwararriyar Mai shirya Abinci kuma mai gabatarwa Fatima Rabi’u Gwadabe, ta ke kawo muku girke-girken Arewacin Nijeriya iri daban-daban da za’a iya gudanarwa a kowanne Dakin Girki. Kowanne shiri yana zuwa mukune da sabon salon girki na musamman daga Arewaci wanda ake gabatarwa cikin sauki da tsari kuma mataki-mataki, dadin dadawa, za’a koyi fasahar girke-girke na gargajiya. Sa’annan, masu kallo zasu san muhimmancin amfani da kayayyakin gina jiki da kuma Sinadaran girki na musamman.
Dadin Kowa.
gyara sasheWasan kwaikwayo na asali mai farin jini da AREWA24 ta shirya, wanda ya lashe lambar yabo, inda ya kawo labarin Dadin Kowa, wani kirkirarren gari wanda jaruman cikinsa suke nuni da irin rayuwar al’ummar dake arewacin Najeriya ta zahiri. Da irin wannan labaran ne masu kallo suke ganin kansu a wannan matsayi da irin burikansu da kalubalensu da kuma kwatanta irin dabi’un su wajen fadi tashinsu wajen yanke shawara game da sana’arsu da iyalansu da kudadensu ko kuma rikici. Dadin Kowa shine ya cinye gasar Afirka Magic na 2016.
Kwana casa'in.
Shiri ne mai kayatar da yan kallo, Wanda ke da masoya masu kallon shi a ko Wani sati. Kirkirarren labari ne Wanda ke nuni Yarda siyasa take.
Rahotanni.
Rahotanin na abun da yake faruwa.
Ubongo Kids
Shiri ne domin Yara,shirin da ke nuna ma raya yarda zasu yi lissafi cikin sauqi.
Mata a yau
Shiri ne domin Mata, Shiri ne da ke duba rayuwar mata, Shiri ne wanda mata jagorancin shi ,shiri ne wanda ake gaiyato Jarumanmun mata sanannu fitattu Dan su ba data su gudunmuwar su, su bada labarin kwagwarmayar da kalubalen dasuka fuskan ta a rayuwar su ta duniya.
Shirin ne da ake karfafa ma mata guiwa a rayuwar su.
Mai ake yayi
Shiri ne da ake nuna Abunda ake yayi a lokacin Kamar su: kayan da ake yayi,wakar da ake yayi,Rawar daake yayi, MOTA da sauran su.
A wanna rana.
Shiri ne ake yi a wanan Rana .Misali: Ranar Yara ta duniya, Ranar Mata na duniya da sauran su.
Al'adun mu.
Shiri ne akan Al'adun mu na hausa , Wanda aka nuna yarda hausawa suke yarda suke ,Suna nuna yarda Abincin su yake, kalan kayan da suke da wasa da Sana'a da suka fiyi da sauran su.
Dandaliln Taurari.
Dandali ne Wanda ake gaiyato Taurarin Kamar:shahararun mawaka da yan fim din kanniwod da manyan Yan TikTok. Wanda shahararun mawaka suka zo kamar haka:
- Nura m Inuwa
- Adam zango
- Umar m shareef
- Yakubu Mummad
- Sani Danja
- Mai dawaiya
- Fati Nijer
- Fantimoti da sauran su