Amina Sadr
Amina Sadr | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kadhimiya (en) , 23 ga Faburairu, 1937 |
ƙasa | Irak |
Mutuwa | Bagdaza, 9 ga Afirilu, 1980 |
Makwanci | Maƙabartar Wadi-us-salam |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Haydar al-Sadr |
Ahali | Muḥammad Bāqir aṣ-Ṣadr (en) |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci da Malami |
Imani | |
Addini | Shi'a |
Amina Haydar al-Sadr ( Larabci: آمنة حيدر الصدر ; 1937 – 1980), Wanda akafi sani da Bint al-Huda al-Sadr ( بنت الهدى الصدر ), malama ce kuma mai fafutukar siyasa a Iraqi wanda Saddam Hussein ya kashe tare da dan uwanta, Ayatullah Sayyid Mohammad Baqir al-Sadr, a shekara ta 1980.
Rayuwarta da aikinta
gyara sasheAn haifi Aminah Haidar al-Sadr a shekara ta 1937 a Kazimiyah, Bagadaza inda a ƙarshe zata kafa makarantun addini da yawa ga 'yan mata. Bint al-Huda ta taka rawar gani wajen wayar da kan al'ummar musulmaikasar Iraki. Tana da shekara ashirin a lokacin da ta fara rubuta labarai a cikin al-Adwaa, mujallar Musulunci da malaman addini na Najaf, Iraki, suka buga a shekara ta 1959. Ta kuma shahara wajen shiga cikin tashin hankalin Safar a shekarar 1977. Bint al-Huda ta girma da tsananin son karatu. Bada jimawa ba sai ta fahimci irin wahalar da matan musulmai suke ciki da kuma manyan bala'o'i da suke cutar da akidun Musulunci a kasarta.
A shekara ta 1980 ne aka kama jagoran addinin Ayatullah Sayyid Mohammad Baqir al-Sadr da 'yar uwarsa Bint al-Huda, inda aka azabtar da su da wulakanci, daga bisani gwamnatin Saddam Hussein ta kashe shesu saboda rawar ganin da suke takawa awajen adawa da gwamnatin. Gwamnati bataa mayar da gawarta ba, amma an ce an binne ta a Wadi Al-Salam, Najaf.
Ayyukanta
gyara sashe- Kalma Da Kira - Littafin farko da aka buga a cikin shekara ta1960s
- Nasara Nagari
- Uwargida Tare Da Annabi
- Mata Biyu Da Namiji - labari game da ilimi da jagora
- Rikicin gaskiya
- Mai Neman Gaskiya - An buga shi a cikin 1979
- Memories Akan Tuddan Makka - An rubuta bayan aikin hajjinta Ito Makka a shekara ta 1973
- Taro A Asibitin
- Goggo ta bata
- Da Ni Amma Nasani
- Wasan
- Jaruman Mata Musulmai
- Muhawara ta Ciki
- The Lost Diary
- Zabar Mata
- Ƙaddara
- Tafiya ta Ruhaniya
- Mugun ciniki
- Kyauta
- Ziyara Zuwa Ga Amarya
- Muhawara ta Ciki
- Kwanakin Karshe
- Lokacin wahala
- Sabuwar Fara
- Sa'o'in Ƙarshe
- Gwagwarmayar Rikici
- Zaman zaman banza
- Rashin godiya
- Tsaya Tsaya
- Wasan Hatsari
- Littafin Diary na Dalibi Musulmi
Duba kuma
gyara sashe- Nosrat Amin
- Zohreh Sefati
- Amina Bint al-Majlisi