Mama Amin
Hajiyeh Seyyedeh Nosrat Begum Amin, wacce akafi sani da Banu Amin, Lady Amin ( Persian shekara ta1886–1983), ita ce fitacciyar mace a Iran masaniyar fikihu, masaniyar tauhidi kuma babbar malama sufi musulma( 'arif ) na karni na 20, Uwargida Mujtahideh . Ta sami ijazah da yawa na ijtihadi, daga cikinsu daga Ayatullah Muḥammad Kazim Ḥusayni Shīrāzī shekara ta (1873-1947) da Grand Ayatullah 'arif shekara ta(1859-1937), wanda ya assasa makarantun Qum ( hawza ). [1]
Mama Amin | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Isfahan, 1886 |
ƙasa | Iran |
Mutuwa | Isfahan, 1983 |
Karatu | |
Harsuna | Farisawa |
Sana'a | |
Sana'a | mystic (en) da Malamin akida |
Imani | |
Addini | Shi'a |
Ta kuma ba wa malamai mata da maza ijaza da dama na ijtihadi, daga cikinsu akwai Sayyid Mar'ashi Najafi . [2]
Ta rubuta litattafai da dama game da ilimin Musulunci, daga cikinsu akwai tafsiri a mujalladi 15, sannan ta kafa makabci a Isfahan a shekara ta 1965, mai suna Maktab-e Fatimah . Babbar dalibar Banu Amin, Zīnah al-Sādāt Humāyūnī (b. Shekara ta 1917) ta jagoranci maktab ɗin tun kafuwarta har zuwa shekara ta 1992. Bayan shekara ta 1992, Hajj Āqā Hasan Imāmi, dangin Humāyūnī, ya kuma karɓi ragamar darakta.
Banu Amin an haifeta agidan 'yan kasuwa. Mijin Nuṣrat Amin shine kawunta Haj Mirza, wanda kuma akafi sani da Muīn al-Tujjar. Anasan mahaifinta da suna Haj Sayyid Muḥammad ‘Ali Amin al-Tujjar. 'Yar uwarsa Hashimiyyah al-Tujjar ita kanta mujtahida ce wacce ta sami digiri na ijtihadi a fiqhu da usūl . Bugu da ƙari, Nuṣrat Amīn tana da ƴa, Iffat al-Zamān Amīn (1912-1977), wanda kuma aka sani da Iftikhār al-Tujjar, wacce ta kasance ɗaya daga cikin fitattun ɗalibanta kuma wacce ta karɓi ijazah na riwaya a Najaf ta Ayatullah Mahmoud Hashemi Shahroudi .
Banu Amin ta haifi ‘ya’ya takwas, daya ne kawai ta rasu acikinsu (Sayyid Muhammad ‘Ali Mu’in Amin). An binne ta a makabartar Takht-e Fulad da ke Isfahan.
Ayyukanta
gyara sashe- al-Arba'in al-Hashimiyyah
- Jā̄mi’ al-shatāt
- Al-Nafaḥāt al-Raḥmaniyyah fi al-Vāridat al-Qalbiyah
- Sayr va Sulūk dar Ravish-i Awliyāʼ-i Allāh
- Akhlaq va Rahi Sa'adat: Iqtibas va tarjamih az Taharat al-Iraqi Ibn Maskuyih.
- Ravish-i Khushbakhtī va Tawīyih bih Khāharān-i Imani
- Makhzan al-‘irfan dar ’ulum-i Qur’an
- Makhzan al-laāli dar fazilat-i mawlá al-mawali hazrat-i Ali ibn Abitalib
- Ma'ad, ya Ākharin Sayr-i Bashar
Labarinta da takardun shaida
gyara sashe- Amū Khalīli, Marjan. Kawkab-i durrī: [sharḥ-i ahvāl-i bānū-ye mujtahidah Amīn], (Tehran: Payām-e `Adālat, 1379 [2000]).
- Bāqiri Bīdʾhindi, Nasir. Bānū-yi nimūnah: gilwahāyī az Haayāt-i bānu-yi mujtahidah Amīn Iṣfahānī, (Daftar-i Tabliqat-i Islāmī-yi Ḥawzah-yi ’ilmīyah-yi - Islamic Propagious Office of the Religious Q. 1382 [2003].
- Tayyibī, Nāhid. Zindagānī-yi Bānū-yi Īrānī: Bānu-yi Mujtahidah Nuṣrat al-Sādāt Amīn, (Qom: Sābiqun Publishers, 1380 [2001]).
- Majmūʻah-ʾi maqālāt wa sukhanrānīhā-yi avvalīn wa duvumīn Kungrih-ʾi Buzurgdāsht-i Bānū-yi Mujtahidah Sayyidah Nuṣrat Amīn (rah), Markaz-i Muṭālaʻāt wa Taḥ-ṭālaʻāt wa Taḥ-ḭātī Fariqā Farhangi-i Bānūwan, Qom, 1995 (1374).
- Yādnāmah-i bānū-yi mujtahidah Nuṣrat al-Sādāt Amīn: mashhūr bih Bānū-yi Īrāni, (Isfahan: Vizārat-i Farhang wa Irshād-i Islāmī; Markaz-i Muṭālaʿātī91 Farhang-19 Farhang [15] ]) .
Kara karantawa
gyara sasheSake dubawa kuma
gyara sasheNassoshi dakarin bayanan kula
gyara sashe- ↑ See ʻAmū Khalīlī, Marjān. Kawkab-i durrī: [sharḥ-i ahvāl-i bānū-ye mujtahidah Amīn], (Tehran: Payām-e ʻAdālat, 1379 [2000]).
- ↑ See Mirjam Künkler and Roja Fazaeli, ‘The Life of Two Mujtahidas: Female Religious Authority in 20th Century Iran’, in Women, Leadership and Mosques: Changes in Contemporary Islamic Authority, ed. Masooda Bano and Hilary Kalmbach (Brill Publishers, 2012), 127-160. SSRN 1884209
- Empty citation (help)
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Tarihin Lady Nusrat Beygum Amin, Al-Islam.org