Amal Umar
Amal Umar (an haifeta a ranar 21 ga watan Octoba, shekarata 1998) a Jihar Katsina, a kasar Najeriya, ta kasance ƴar wasan kwaikwayo ce a masana'antar fim ta Kannywood. Ta kuma fito a cikin shirin turanci na Nollywood MTV Shuga Naija tare da sauran taurarin Hausa, kamarsu Rahama Sadau da Yakubu Muhammed.[1][2]
Amal Umar | |
---|---|
Rayuwa | |
Karatu | |
Makaranta | Yusuf Maitama Sule Un AUWALI SANI BENA (en) |
Harsuna |
Hausa Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da ɗan wasan kwaikwayo |
Kuruciya da Ilimi
gyara sasheAn haifi Amal, ranar 21 ga watan Oktoba a shekara ta 1998 a jihar Katsina, kasar Najeriya. Tayi karatun ta na firamare da sakandare a Katsina, sannan ta koma jihar Kano domin yin karatun gaba da sakandare a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano.
Sana'a
gyara sasheAmal Umar ta fara wasan kwaikwayo ne a shekara ta 2015, inda ta shiga masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood. Amma kafin ta fito a fim ta fara fitowa cikin bidiyon waƙoƙi tare da mawaƙa kamar Umar M Sherrif, Garzali Miko da sauransu. Ta fara fitowa a fim ɗin Hausa mai suna "Itikam" tun daga nan ta fara samun suna a faɗin ƙasar Hausa. Ayyukanta sun fara haskakawa bayan fitowarta ta farko a cikin jerin matasan Nollywood MTV Shuga.
Manazarta
gyara sashe- ↑ saharan1 (2021-12-13). "Amal Umar Biography Acting Career Awards Latest Pictures". S-News (in Turanci). Archived from the original on 2022-07-31. Retrieved 2022-07-31.
- ↑ "Shuga" MTV Shuga Naija - Ep 4 (TV Episode 2019) - IMDb (in Turanci), retrieved 2022-07-31