Jami'ar Yusuf Maitama Sule

Jami'ar Najeriya

Jami'ar Yusuf Maitama Sule Kano, tsohon sunan ta na da Northwest University Kano Jami'a ce mallakin gwamnatin jahar Kano mai mazaunin wucin gadi a tsakiyar birnin na Kano da kuma mazaunin dindindin a kan titin Gwarzo cikin birnin na Kano. Tana daga cikin jami'o'in da suka kafu a shekarar 2012 kuma tasamu amincewar hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa wato NUC. [1]

Jami'ar Yusuf Maitama Sule

Knowledge for self reliance and development
Bayanai
Iri jami'a
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 2012
yumsuk.edu.ng
Ginin jami'ar na wucin gadi
Ginin Jami'ar na dindindin
Yusuf Maitama University

Jami'ar ta Yusuf Maitama Sule University, Kano an ƙirƙireta a shekarar 2012 lokacin gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso domin bunƙasa tsohuwar jahar Arewa maso Yammacin Najeriya kuma aka yi mata laƙani da North-West University wato Jami'ar Arewa maso Yamma. Sai dai daga baya Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta canza sunan Jami'ar zuwa Yusuf Maitama Sule University domin girmamawa ga Tsohon sanannen ɗan siyasar nan na Najeriya kuma babban dattijon ƙasar wato marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule. An kafa Jami'ar ne domin bunƙasa ilimi ba kawai a yankin na Arewa maso yamma ba harma da ƙasar daba Nahiyar Afrika baki daya.

Manazarta

gyara sashe