An nada Laftanar Kanar (daga baya Birgediya) Umaru Mohammed Gwamnan Jihar Arewa maso Yamma a Najeriya a watan Yulin shekara ta 1975 a farkon mulkin soja na Janar Murtala Mohammed . A watan Fabrairun shekara ta 1976 an raba Jihar Arewa maso Yamma zuwa Jihar Neja da Jihar Sakkwato . Umaru Mohammed ya ci gaba da zama Gwamnan Jihar Sakkwato har zuwa Yulin shekara ta 1978.

Umaru Mohammed
gwamnan jihar Sokoto

ga Maris, 1976 - ga Yuli, 1978
Usman Faruk - Muhammad Gado Nasko
Rayuwa
Haihuwa Hadejia
ƙasa Najeriya
Mutuwa 26 Mayu 1980
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Digiri Janar

Umaru Mohammed ya rasu ne a ranar 26 ga watan Mayun shekara ta 1980 a wani hatsarin jirgin saman Fokker F27 na sojojin sama akan hanyar zuwa Sao Tomé da Principe a wani aikin diflomasiyya. Ya kasance yana tafiya ne a madadin kwararren abokinsa Ibrahim Babangida, wanda aka amince da shi ya tafi Amurka don horar da kwararru.[1] [2]

Manazarta gyara sashe

  1. "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2010-01-06.
  2. Nowa Omoigui. "Barracks: The History Behind Those Names". Dawodu. Retrieved 2010-01-06.