Transsion

Kamfanin Chaina na ƙera wayoyin hannu

Transsion Holdings ( Chinese ) wani kamfani ne na ƙasar Sin/Chaina mai ƙera wayoyin hannu da ke birnin Shenzhen. Shine kamfanin ƙera wayoyin salula mafi girma ta hanyar tallace-tallace a Afirka a cikin 2017, kuma yana sayar da wayoyin hannu a Gabas ta Tsakiya, Kudu maso Gabashin Asiya, Kudancin Asiya, da Latin Amurka. Alamomin sa sun haɗa da samfuran waya irin su Itel, Tecno, Infinix ; alamar sabis na bayan-tallace-tallacen Carlcare; da na'urorin haɗi Oraimo. Yana ƙera wayoyi a China, Pakistan, Ethiopia, Bangladesh da kuma kwanan nan a Indiya.

Transsion
Bayanai
Suna a hukumance
深圳传音控股有限公司
Iri kamfani
Masana'anta consumer electronics (en) Fassara
Ƙasa Sin
Aiki
Ƙaramar kamfani na
Kayayyaki
Mulki
Hedkwata Shenzhen
Tarihi
Ƙirƙira 2006
transsion.com

Transsion Holdings Pvt Ltd an kafa shi azaman (Transsion Technology) a Hong Kong a cikin 2006, tare da mai da hankali kan haɓakawa, samarwa, tallace-tallace, da sabis na samfuran sadarwar wayar hannu. Da farko kamfanin Transsion ya shigo da wayoyin hannu a kasuwannin Afirka tare da samfuran Tecno da Itel, kuma ya fara mai da hankali kan kasuwannin Afirka a cikin watan Yuli, shekara ta 2008.[1] Kamfanin Transsion ya fitar da wayarsa ta farko a cikin shekara ta 2014.[2]

Transsion ya kafa reshensa na Najeriya a watan Yunin 2008, kuma yana da rassa a kasashe bakwai na Afirka a watan Oktoban wannan shekarar.[1] Transsion ya kafa masana'anta a Habasha a cikin 2011.[3] Transsion ya shiga kasuwar Indiya a cikin shekara ta 2016.[2] Kasuwannin kamfanonin wayar salula na kamfanin Transsion a Afirka idan aka haɗe sun zarce na kamfanin Samsung a shekarar 2017, abin da ya sa Transsion ya zama mafi girma wajen ƙera wayoyin komai da ruwanka a kasuwannin Afirka a kashi na huɗu na shekarar 2017.[4][5] Transsion ya kasance kamfani mafi girman ƙera wayoyin hannu a Afirka a farkon rabin shekarar 2017.[6] Ƙoƙarin kamfanin Transsion a shekara ta 2018 na Reverse takeover ya ci tura.[7] A cikin Oktoba 2018, Transsion Holdings sun fara ƙera wayoyin hannu a sabuwar masana'antar su a Bangladesh.[8] Transsion Holdings ya zama kamfani da aka jera na jama'a a watan Satumbar 2019 ta jeri akan sashin Kasuwar STAR na Kasuwancin Hannun Jari na birnin Shanghai.[9]

Kamfanin na Transsion yana sayar da wayoyin hannu a nahiyoyin Afirka, Gabas ta Tsakiya, Kudu maso Gabashin Asiya, Kudancin Asiya, da Latin Amurka.[6] Yana aiki da alamun wayar hannu samfuran Tecno, Itel, da Infinix, da kuma bayan-tallace-tallace sabis na goyon bayan Carlcare da na'urorin haɗi Oraimo[4] Spice Digital, alamar wayar Indiya, an samo shi a cikin 2017.[2] Transsion na ƙera wayoyinsa a China, Habasha, Bangladesh, Indiya, Pakistan.[10] Transsion ne kamfanin wayar hannu na farko da ba na Afirka ba, da ya kafa hanyar sadarwar talla dake taimakon tallace-tallace a Afirka.[3]

Nasarar da kamfanin Transsion ya samu a kasuwannin Afirka ana alaƙanta shi da daidaita fasalin wayoyinsa da bukatun kasuwannin Afirka.[4] Wayoyin Transsion suna ba da fasalin da ke daidaita fidda kyamara don sautunan fata masu duhu, yana ba da damar adana bayanan fuska. Transsion ya haɓaka wayoyi masu aikin SIM biyu, waɗanda suka sami karɓuwa sosai saboda masu amfani yan Afirka galibi suna amfani da katin SIM fiye da ɗaya a lokaci ɗaya don adana kuɗi. Transsion ya fitar da wayoyin da batiran su kan ɗauki dogon Zango-(batare da canjin ya ƙare da wuri ba), waɗanda suka dace da karancin wutar lantarki da Afirka ke fama da ita.[1][2][4] Har wayau wayoyin an tsara su ga yarurruka ko harsunan Afirka da yawa, kuma Tecno ita ce babbar alama ta wayar hannu ta farko a Habasha da ta haɗa da samfurin madannai na Amharic.[3] Transsion na tallata nau'ikan wayoyin hannu a Afirka.[1][2]

Baya ga nasarorin da kamfanin ya samu a kasuwannin Afirka, Transsion na ɗaya daga cikin kamfanonin wayar salula mafi girma a Indiya, tare da karuwar YoY da kashi 40% a shekarar 2019. Har ila yau, ita ce tambari lamba ɗaya a cikin kasuwar wayoyin salula na zamani.[11]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 韓, 江雪 (24 August 2018). "傳音手機:非洲手機市場的封王之路". PEdaily.cn (in Harshen Sinanci). Retrieved 2 January 2019.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 "「非洲之王」传音:出海手机厂商的另类封王之路". Geekpark (in Harshen Sinanci). 1 March 2018. Retrieved 2 January 2019.
  3. 3.0 3.1 3.2 陈, 伊凡 (11 November 2018). "坚挺十多年,隐藏在非洲的中国手机巨头". PEdaily.cn (in Harshen Sinanci). Retrieved 4 January 2019.
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 Dahir, Abdi Latif (30 August 2018). "A low-profile, Chinese handset maker has taken over Africa's mobile market". Quartz Africa. Retrieved 4 January 2019.
  5. Manek, Sheila (12 March 2018). "Africa's Smartphone Market Declines Despite Strong Performance of Region's Biggest Markets". IDC. Archived from the original on 31 May 2019. Retrieved 5 January 2019.
  6. 6.0 6.1 Hancock, Tom (19 November 2017). "China's Transsion dominates African mobile phone market". Financial Times.
  7. 石, 飞月 (19 June 2018). "重组失败 传音能否"走出非洲"". Beijing Business Today (in Harshen Sinanci). Archived from the original on 6 January 2019. Retrieved 6 January 2019.
  8. "深圳传音控股股份有限公司". www.transsion.com. Archived from the original on 2020-07-13. Retrieved 2020-07-11.
  9. "Transsion, maker of TECNO & Infinix smartphones, is now a public listed company". MobiTrends Kenya - Smartphones & Tech News (in Turanci). 2019-09-30. Retrieved 2020-07-11.
  10. 賴, 瑩綺 (21 November 2017). "大陸隱形冠軍 傳音手機 在非洲銷量第1". China Times (in Harshen Sinanci). Retrieved 2 January 2019.
  11. Jain, Anshika (24 October 2019). "India Smartphone Shipments Reached a Record-High 49 Million units Defying the Economic Slowdown Trends in Other Sectors". Counterpoint Research. Archived from the original on 8 November 2019. Retrieved 11 December 2019.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe