Tecno Mobile
Tecno Mobile kamfanin ƙera wayoyin hannu ne na ƙasar Sin da ke Shenzhen, China.[1] An kafa shi a shekara ta 2006. Wani reshe ne na Transsion Holdings.
Tecno Mobile | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ƙaramar kamfani na |
Masana'anta | consumer electronics (en) |
Aiki | |
Kayayyaki | |
Mulki | |
Hedkwata | Shenzhen |
Mamallaki | Transsion Holdings |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2006 |
Wanda ya samar |
George Zhu (en) |
|
Kamfanin na Tecno ya mayar da hankali kan kasuwancinsa a majiyoyin Afirka, Gabas ta Tsakiya, Kudu maso Gabashin Asiya, Kudancin Asiya, Latin Amurka, da kasuwannin Gabashin Turai.
Tarihi
gyara sasheA cikin shekara ta 2006, an kafa kamfanin Tecno Mobile a matsayin Tecno Telecom Limited, amma daga baya ya canza suna zuwa Transsion Holdings tare da Tecno Mobile yana aiki a matsayin ɗaya daga cikin rassansa. A cikin 2007, kamfanin Tecno ya ƙirƙiri tambari na biyu, Itel wanda aka sayar a Afirka. A farkon 2008, Tecno ya mayar da hankali ga Afirka gaba ɗaya bayan binciken kasuwa, kuma zuwa 2010, yana ɗaya daga cikin manyan samfuran wayar hannu guda uku a Afirka.[2]
A cikin 2016, Tecno ya shiga dillancin wayar hannu na kamfanin a Gabas ta Tsakiya.[3] A cikin 2017, ya shiga kasuwannin Indiya, inda ya ƙaddamar da samfurin wayoyinsa na 'Made for India': jerin 'i' - i5, i5 Pro, i3, i3 Pro da i7. Kamfanin ya fara dillancin sa a jihohin Rajasthan, Gujarat, da Punjab, kuma a watan Disamba 2017 ya bazu a faɗin kasar.
Kamfanin ya gano wasu kasuwanni masu tasowa, ban da Afirka da Indiya, masu yawan jama'a amma akwai ƙarancin cinikayya hajar sa a wuraren. Har wayau bai tsaya nan ba, ya kutsa kasuwannin Bangladesh da Nepal a cikin 2017 kuma ya fara gwajin sayar da hajarsa a Pakistan.[4] Har yanzu kamfanin na ƙoƙarin kutsawa cikin kasuwar Pakistan kuma ya fara siyar da hajarsa ta yanar gizo-(online) ta hanyoyin kasuwanci ta Intanet-(E-commerce).
Wayoyin da ake ƙerawa
gyara sasheWayoyin hannu na Tecno da ake sayarwa a Indiya, ana ƙera su a masana'antar Noida (U.P.).[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Deck, Andrew (2020-06-23). "Your guide to Transsion, Africa's biggest mobile phone supplier". Rest of World (in Turanci). Retrieved 2020-08-08.
Transsion operates three brands from its headquarters in Shenzhen in China: Infinix, Itel, and Tecno.
- ↑ "Samsung, Apple, Tecno top list of mobile brands with highest SOV in Q2 of 2016" (in Turanci). Archived from the original on 2022-10-01. Retrieved 2017-08-26.
- ↑ "Chinese phone maker Tecno Mobile forays into Middle East". Retrieved 1 October 2017.
- ↑ "How Transsion became No 3 in India by solving oily fingers problem". South China Morning Post (in Turanci). Retrieved 2018-01-15.
- ↑ "Transsion Holdings to shift manufacturing base to India".