Thomas Jefferson
Thomas Jefferson (an haife shi ranar 13 ga watan April, shekarar 1743 – ya mutu a ranar 4 ga watan July, shekarar 1826) Yakasance daya daga cikin shugabannin kasar Tarayyar Amurka, diplomat, lauya, architect, kuma daya daga cikin Iyayen da suka kafa Tarayyar Amurka wanda shine na uku shugaban Tarayyar Amurka daga shekarar 1801 zuwa shekara ta 1809. Kafin nan, ya riƙe mataimakin Tarayyar Amurka daga shekarar 1797 zuwa shekara ta 1801. Shine wanda ya wallafa Declaration of Independence, Jefferson was a proponent of democracy, republicanism, da yancin mutane, ya tunzura American colonists da rabewa daga Kingdom of Great Britain da samar da sabuwar ƙasa; ya samar da littafai tsarin shugabanci da ƙuduri a matakin jiha da kuma tarayya.
Lokacin American Revolution, ya wakilci Virginia a Continental Congress wanda suka fara amfani da kundin da ya samar, ya kuma fara dokar yancin yi addini amatsayin sa na wakili daga Virginia, kuma yazama Governor of Virginia na biyu daga shekarar 1779 zuwa shekara ta 1781, lokacin American Revolutionary War. Yazama Ministan Tarayyar Amurka na Faransa a watan Mayu shekarar 1785, kuma shine na farko wanda ya rike muƙamin secretary of state a karkashin shugaba George Washington daga 1790 zuwa 1793. Jefferson da James Madison su suka shirya Democratic-Republican Party domin tayi hamayya da Federalist Party lokacin tsara First Party System. Tareda Madison, ya rubuta Kentucky and Virginia Resolutions a shekarar 1798 da shekara ta 1799, wanda ke tsoron kara karfin states' rights da soke Alien and Sedition Acts na fedaraliya.