Open main menu

Italiyanci yare ne wanda Turawan ƙasar Italiya (Italy) suka fi yawan magana da shi. Hakazalika, ana amfani da shi a matsayin yaren gwamnati a kasar Italiya da kasar Switzerland, San Marino da kudancin Istriya dake ƙasar selvoniya Kroatiya kuma ana magana da harshen Italiyanci sosai a Albaniya, Malta, Monaco da kuma wasu ɓangarori na ƙasar Faransa (musamman a cikin garuruwan Dodecanese) Montenegro (Kotor), da wasu ɓangarori ƙasar Girka (a tsibirin Ionian da Dodecanese). Harshen Italiyanci ya taka muhimmiyar rawa a ƙasashen arewacin Afrika da kuma gabashin Afrika kuma ana amfani da harshen Amurka da Austaraliya akwai mutanen marasa rinjaye da kuma suke amfani da harshen a ƙasashen Bosnia Herzegovina, Kroatiya , Sloveniya da Romainiya.

Wannan ƙasida guntu ne: yana buƙatar a inganta shi, kuna iya gyarashi.