Oserheimen Osunbor
Oserheimen Osunbor, (an haife shi ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 1951), lauyan Najeriya ne kuma ɗan siyasa wanda ya kasance Sanatan Tarayyar Najeriya daga ranar 29 ga watan Mayun shekarata 1999 zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2007 kuma gwamnan jihar Edo na Najeriya daga ranar 29 ga watan Ma Mayun 2007 zuwa ranar 11 ga watan Nuwamban 2008.[1]
Oserheimen Osunbor | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Bangare na | Nigerian senators of the 4th National Assembly (en) da Nigerian senators of the 5th National Assembly (en) |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Sunan asali | Oserheimen Osunbor |
Sunan haihuwa | Oserheimen Osunbor |
Shekarun haihuwa | 5 Oktoba 1951 |
Yaren haihuwa | Harshen Esan |
Harsuna | Turanci, Harshen Esan da Pidgin na Najeriya |
Writing language (en) | Turanci |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | Gwamnan jahar Edo, mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar dattijai ta Najeriya |
Ilimi a | Makarantar Koyan Lauya ta Najeriya da Jami'ar Najeriya, Nsukka |
Ɗan bangaren siyasa | Peoples Democratic Party |
Ƙabila | Mutanen Esan |
Eye color (en) | brown (en) |
Hair color (en) | black hair (en) |
Mabiyi | Lucky Igbinedion |
Wanda ya biyo bayanshi | Adams Aliyu Oshiomhole |
Kyauta ta samu | Tallafin karatu na Rhodes |
Personal pronoun (en) | L485 |
Rayuwar farko da aiki
gyara sasheAn haifi Oserheimen Osunbor a ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 1951 a Iruekpen, ƙaramar hukumar Esan ta Yamma, jihar Edo, Najeriya. Ya halarci makarantar firamare ta PTTC Igueben daga shekarar 1957 zuwa 1962, sannan ya halarci makarantar Anglican Grammar School Ujoelen Ekpoma daga shekarar 1963 zuwa 1968 sannan ya samu fom na shida a Holy Trinity Grammar School Sabongidaa-Ora Edo State. [ana buƙatar hujja]
Ofishin Sanata
gyara sasheAn zaɓi Farfesa Oserheimen Osunbor a matsayin Sanata mai wakiltar Edo ta tsakiya a jihar Edo a Najeriya a farkon jamhuriya ta huɗu a jam'iyyar People's Democratic Party (PDP). Ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayun 1999.[2] Bayan ya hau kujerar majalisar dattawa a cikin watan Yunin shekarar 1999 aka naɗa shi a kwamitocin kan dokoki da ƙa'idoji, da'a, shari'a, albarkatun ruwa da harkokin gwamnati (Chairman).[3] An sake zaɓen Osunbor a kujerar Sanata a cikin watan Afrilun shekarata 2003.[4] Ya kuma riƙe muƙamai daban-daban na shugaban ƙasa yayin da yake Majalisar Dattawa da suka haɗa da: Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC); Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai kan Shari’a, Ƴancin Ɗan Adam da Al’amuran Shari’a; Shugaban kwamitin majalisar dattawa da dama da kwamitocin haɗin gwiwa na majalisar dokokin ƙasa; Shugaban, Ƙaramin Kwamitin Majalissar dokoki da Lissafin Majalisu, Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki. Tasirinsa ya yi zurfi sosai har abokan aikinsa suka yi masa laƙabi da "Attorney-General of the Senate".[ana buƙatar hujja]
Gwamna
gyara sasheAn zaɓi Osunbor a matsayin gwamnan jihar Edo a Najeriya a cikin watan Afrilun shekarar 2007 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.[5] A ranar 20 ga watan Maris ɗin 2008, Kotun Zaɓen Gwamnan Jihar Edo ta bayyana cewa zaɓen Osunbor bai yi nasara ba, kuma ta nemi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da ta janye satifiket ɗinsa ta bayyana Adams Aliyu Oshiomhole na jam’iyyar Action Congress (AC) a matsayin wanda ya lashe zaɓen.[6] A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2008, wata kotun ɗaukaka ƙara ta tarayya da ke zama a birnin Benin, ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a jihar, inda ta bayyana Oshiomole a matsayin gwamnan jihar Edo. An yanke shawarar ne bisa wasu kura-kurai da aka samu a zaɓen.[7]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheOserheimen Osunbor ya yi aure cikin farin ciki tare da ƴaƴa shida. Shi Kirista ne na ɗarikar Anglican kuma Knight na Saint Christopher[ana buƙatar hujja]
Duba kuma
gyara sashe- Jerin Gwamnonin Jihar Edo
Manazarta
gyara sashe- ↑ http://psephos.adam-carr.net/countries/n/nigeria/nigerialeg2.txt
- ↑ http://psephos.adam-carr.net/countries/n/nigeria/nigerialeg2.txt
- ↑ https://web.archive.org/web/20091118151316/http://www.nigeriacongress.org/assembly/committees1.htm
- ↑ http://www.dawodu.com/senator.htm
- ↑ https://www.worldstatesmen.org/Nigeria_federal_states.htm
- ↑ https://allafrica.com/stories/200803210465.html
- ↑ Governor's Election Nullified". Africa Research Bulletin: Political, Social and Cultural Series. Blackwell. 45 (3): 17419C. 2008. doi:10.1111/j.1467-825X.2008.01568.x.