Nyaknno Osso ma'aikacin Laburare ne, ɗan jarida, kuma shi ne wanda ya kafa Gidauniyar Legacy da Bincike (BLERF).[1][2]

Nyaknno Osso
Rayuwa
Haihuwa Jahar Akwa Ibom, 27 ga Augusta, 1954 (70 shekaru)
ƙasa Najeriya
Mazauni Jahar Ibadan
jahar Port Harcourt
Kogin Cross River (Najeriya)
Ogun
Abuja
Ƴan uwa
Abokiyar zama Emem (en) Fassara
Angela
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Matakin karatu Doctor of Philosophy (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a editor-in-chief (en) Fassara, librarian (en) Fassara, researcher (en) Fassara da babban mai gudanarwa
Wurin aiki News Watch 9 (en) Fassara
Employers Olusegun Obasanjo Presidential Library
Imani
Addini Kiristanci

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

Nyaknno Osso ya ƙare karatun digiri daga Jami'ar Ibadan (Makarantar Laburare, Ajin 1975) [3]

Ayyukan sana'a wanda Mista Osso ya ƙare akai sun haɗa da aikin ɗakin karatu a Jami'ar Ibadan daga 1971-75 da kuma aikin gwamnati a matsayin babban ma'aikacin laburare da kuma mai bincike a Kamfanin Jaridun Jihar Kuros Riba daga 1975 zuwa 1984. [4] [5][3]Ya koma Mujallar Newswatch a shekarar 1984, anan ya dauki matsayin babban ma'aikacin gudanarwa na farko tare da Dele Giwa da Ray Ekpu, [4] daga ƙarshe ya hau muƙamin Shugaban Bincike. Bayan kammala aikinsa a cikin 1991, sa'annan ya ɗauki matsayin mai ba da shawara a kan laburare a cikin Newswatch, inda daga baya ya zama editan Newswatch na bikin "Wane ne Wane a Najeriya."[6]

A tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, Mista Osso ya yi aiki a matsayin mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a fannin Laburare, Bincike da kuma hadehaden Takardu.[7][8] A shekarar 2007, a karshen mulkin mai gidansa, ya zama Babban Sakatare kuma Kodinetan Ayyuka na Gidauniyar Dakin karatun shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo (OOPLF).[9] Zamansa a OOPLF ya kare a watan Maris 2013.

Nasarar sana'a

gyara sashe

Nasarorin da Mista Osso ya samu a harkar bincikensa da rubutattun bayanai a Najeriya sune kamar haka: Kafa dakin karatu na jarida a Cross River Media Corporation, Calabar, tun daga 1975 zuwa 1984.[4][10] Laburaren Bincike na Newsmedia a Mujallar Newswatch, da ke Ikeja, Legas, ta yi aiki daga 1984 zuwa 1998, [4] tare da buga Encyclopediar Tarihin Rayuwar yan Nigeria (Newswatch), mai take "Wane ne wane a Najeriya?" a shekarar 1990,[11][3] da yunƙuri da tsare tsare da kuma haɗin gwiwa sa da tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, don gabatar da ɗakin karatu na farko na shugaban kasa a Afirka, ɗakin karatu na Olusegun Obasanjo.[12][13] Nasarar buga rubuce-rubucen Dele Giwa, ɗan jarida ɗan Najeriya na farko da ya kai ga kisan gilla ta hanyar wasiƙar bam, a ƙarƙashin taken "Parallax Snaps: Rubutun Dele Giwa (1998).[4][14]

Kyaututtuka da karramawa

gyara sashe

A cikin watan Satumba na shekarar 2022, Jami'ar Afirka ta Amurka ta ba shi lambar girmamawa ta alfarmar Doctor of Philosophy (PhD).

  1. "Nyaknno Osso: Driving the BLERF Project – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Archived from the original on 2023-02-04. Retrieved 2023-02-04.
  2. Daniel, Soni (22 May 2018). "Nigeria's first online biographical work debuts". Vanguard. Samfuri:ProQuest. Missing or empty |url= (help)
  3. 3.0 3.1 3.2 Empty citation (help) Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 "NYAKNNO OSSO: CELEBRATING A PATHFINDER - THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com (in Turanci). Retrieved 2024-01-26.
  5. "An Insight into Nigeria's Maiden Biographical Encyclopedia". This Day. 17 October 2018. Samfuri:ProQuest. Missing or empty |url= (help)
  6. "Who's who in Nigeria / editor, Nyaknno Osso - Catalogue | National Library of Australia". catalogue.nla.gov.au (in Turanci). Retrieved 2024-01-26.
  7. "Buhari rejoices with renowned Librarian, Nyaknno Osso at 68". The Sun. 26 August 2022. Samfuri:ProQuest. Missing or empty |url= (help)
  8. Ukim, Utibe (8 August 2023). "NyaknnoAbasi Osso: The search engine before Google". Vanguard Media Limited, Nigeria. Retrieved 2024-01-28.
  9. "Nyaknno Osso and BLERF: This idea must not die, By Sam Akpe". Premium Times. 27 August 2022.
  10. "Merchants of the word". The Guardian. 25 November 2021. Samfuri:ProQuest. Missing or empty |url= (help)
  11. "An Insight into Nigeria's Maiden Biographical Encyclopedia". This Day. 17 October 2018. Samfuri:ProQuest. Missing or empty |url= (help)
  12. "Nyaknno Osso: Driving the BLERF Project". This Day. 4 January 2022. Samfuri:ProQuest. Missing or empty |url= (help)
  13. "INTERVIEW: I 'sold' idea of presidential library to Obasanjo - Nyaknno Osso". Premium Times. 28 September 2019. Samfuri:ProQuest. Missing or empty |url= (help)
  14. "Nyaknno Osso: Entrenchment at the mountaintop, By Chuks Iloegbunam". Premium Times. 27 August 2022. Samfuri:ProQuest. Missing or empty |url= (help)