Nura M Inuwa
Nura Musa Inuwa, Ana kiran shi da Nura ko kuma M inuwa, An haife shi ne a ranar 18 ga watan satumba shekara ta alif dari tara da tamanin da tara 1989, a cikin garin Kano, a cikin garin Gwammaja a ƙaramar hukumar Dala.[1][2] ya kasance mawakin hausa, mai rubuta wake, kuma furodusan fim a masana'antar Kannywood. Nura m inuwa Mawakine mai hikima gamida azanci.
Nura M Inuwa | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Dala, Nigeria, 18 Satumba 1989 (35 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Hausa |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Hausa Larabci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Wakoki.
gyara sasheAisha humaira, Rai-dai, Badi ba rai, Soyayyar facebook, Sayyada, Mijin biza, Abinda yake Ruhi, Alkuki, Yan kudu, Zurfin ciki, Soyayyace, Faggen soyayya, inka iya zance, Ga wuri ga waina, Ummi, Uwar mugu Babban gida, Dan gwamna, Manyan mata, Hubbi, Matan zamani, Dan baiwa, Basaja, Zurfin ciki, Abbana, Alkawari, Dawo dawo, Wata ruga, Yar fulani, Salma, Mai gadan zinari, Labarina, Yan arewa, Duniyar masoya, Mailaya, In ka'iya zance, Daren Alkhairi Soyyayya Ruwan zuma, Uwar Amarya Nabiyo Haske Matan Gida.[3]
Kambu da Lamban Girma.
gyara sasheKundin Wakoki.
gyara sashe- Rigar aro
- Wasika
- Dan magori
- Makashinka
- Afra
- Siyan baki
- Matan gida
- Soyayya
- Ranar aurena
- Ma'aurata.
- Mai sauraro
- Ni daku
- Lokaci
- Ango da sauransu.
Daukakar Sa
gyara sasheYa fara waka a shekarar 2007 ya fara ne da waƙar siyasa amma nasararsa tafara ne daga shekarar 2010.
Mawakin nayin salon wakokin siyasa, aure, zauranci, soyayya da kuma wakokin finafinan shirin kannywood.
Wasu wadanda ba asan ko suwayeba Sun wasa masa ruwan acid a shekarar 2012.
Nura yayi waka tare mawaka dayawa kamarsu Umar m sharrit, Billio, Ali show dade sauransu sanan a wakarsu ta siyasa a shekarar 2015 yayi hadaka da mawakan siyasa na arewa Irinsu Rara, Aminu ala, hussaini danko, Adam a Zango, Ali jita, Nazifi Asnanik, Dade sauransu. Kawo yanzu mawakin Yayi wakoki da suka Kai 550 wacce yafiso itace rigar aro.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-08-30. Retrieved 2019-12-23.
- ↑ https://hausa.legit.ng/amp/1101084-dandalin-kannywood-shahararren-mawaki-nura-m-inuwa-zai-angwance.html&ved=2ahUKEwj7h9D3kcbmAhUCyxoKHfDWDoAQFjAMegQICBAB&usg=AOvVaw0BbJrtsWq7_JXNBurrsPNA&cf=1[permanent dead link]
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/amp/labarai-46693772&ved=2ahUKEwj7h9D3kcbmAhUCyxoKHfDWDoAQFjAKegQIBBAB&usg=AOvVaw3iEVIXZHda-89PFwZ1Rsvr&cf=1[permanent dead link]