Nahiya na nufin sashe-sashe ko kuma manya-manyan shigifun da'irar shimfiɗaɗɗiyar ƙasa da ake da su a wannan duniya tamu. Babu dai wata ƙididdiga da ta tabbatar da adadin nahiyoyin da ake da su a duniya baki ɗaya, sai dai kawai ana ganin ko dai guda shida ne ko kuma guda bakwai.

Wikidata.svgnahiya
Continentes Wikipedia.svg
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na landmass (en) Fassara da natural geographic object (en) Fassara
Bangare na Earth's crust (en) Fassara da Duniya
Ƙasantuwa a yanayin ƙasa continental crust (en) Fassara
Shafin yanar gizo whosonfirst.org…
Hannun riga da ocean (en) Fassara

Amma dai abin da aka fi haƙƙaƙewa akai shi ne, waɗannan nahiyoyi guda Bakwai ne. Kuma sun haɗar da Afirka da Antarctica da Asiya da Austaraliya da Turai da kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka. Wannan a yadda aka karantar da ɗalibai kenan a yankin nahiyar Amirka baki ɗaya.

Amma kuma a yankin nahiyar Turai da kuma sauran sassan duniya, mafi yawan ɗaliban yankunan ana karantar da su cewar, nahiyoyi Shida rak ake da su a duniyar nan. Ma'ana a waɗannan yankuna ana duban Kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka a matsayin nahiya guda ɗaya ta Amirka. Anan lissafin nahiyoyi shidan kenan ya haɗar da Afirka da Amirka da Antarctica da Asiya da Australiya da kuma Turai.

To sai dai a halin da ake ciki kuma, mafiya yawan masana ta fuskar kimiyya na duban waɗannan nahiyoyi Shida da cewar nahiyar Turai da ta Asiya a dunƙule suke wuri ɗaya a matsayin nahiya guda, don haka ne ma suke kiran nahiyar da suna Eurasiya, sai kuma Afirka da Antarctica da Austaraliya da Kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka.

Masana ilimin taswirar duniya, su kuma a halin yanzu sun kasafta duniyar nan zuwa yankuna takwas domin samun sauƙin fahimta. Yanki na farko dai shi ne na Asiya, wanda ya ƙunshi Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka. Sai kuma Turai da Arewacin Amirka. Akwai kuma Tsakiyar Amirka da yankin Carribbean. Kana ga Kudancin Amirka da Afirka da Austaraliya da kuma Yankin Teku, wato Oceania kenan.

Nahiyoyi sun haɗa da Afirka da Antatika da Asiya da Osheniya da Turai da Amurka ta Kudu da kuma Amurka ta Arewa.

Yawan jama'aGyara

Continents of the world[1]
Nahiya Faɗin ƙasa Jumullar Mutane
km² mi²
Asiya 44,579,000 17,212,000 4,298,723,000
Afrika 30,221,532 11,668,599 1,110,635,000
Amurka ta Arewa 24,709,000 9,540,000 565,265,000
Amurka ta Kudu 17,840,000 6,890,000 406,740,000
Antatika 14,000,000 5,400,000 4,490 (Estimated)
Turai 10,180,000 3,930,000 742,452,000
Osheniya 8,525,989 3,291,903 38,304,000
Duniya Around 7.7 billion

(As of 2019)

Nahiya mafi yawan mutane itace Asiya, sai Afrika mai biye mata baya. Ta uku itace Turai. Ta huɗu itace Amurka ta Arewa sai ta biyar kuma [[Amurka ta Kudu]].[2]

ManazartaGyara

  1. "Map And Details Of All 7 Continents". worldatlas.com. Retrieved 6 March 2016.
  2. "These maps show where the world's youngest and oldest people live". Public Radio International.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.