Martha Bodunrin (an haife ta a shekara ta 1952) ƴar, siyasar Nijeriya ne. Ta kasance memba na Jam'iyyar Democrat ta Jama'a da Majalisar Wakilai.[1]

Martha Bodunrin
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
Gyang Dalyop Datong - Simon Mwadkwon
District: Barkin Ladi/Riyom
Rayuwa
Haihuwa Jos, 1952 (71/72 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Malami
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Rayuwa gyara sashe

An haifi Bodunrin a cikin 1952. Ta cancanci zama malaai a shekarar 1971.

Ta shiga Jam'iyar Demokradiyyar Jama'a kuma ta kasance ƴar takarar su. A shekarar 2010 ta kasance ƴar majalisar wakilai lokacin da kisan kiyashi ya faru a kauyukan da ke kusa da garin Jos . Ɗaruuruwa sun mutu lokacin da aka kashe manya da yara. Bodunrin ya kwatanta tashin hankali da kisan kare dangin na Ruwanda.

A shekarar 2011 aka sake zaɓarta a Majalisar Wakilai . Sauran matan da aka zaba a wannan shekara sun hada da Folake Olunloyo, Maimunat Adaji, Suleiman Oba Nimota, Betty Okogua-Apiafi, Rose Oko da Nkoyo Toyo .

Kisan kiyashin ya ja hankalin duniya kuma Bodunrin ta zama ƙwararriyar shaida. Bodunrin ta tsunduma cikin neman majalisar don girmama yarjejeniyar da ta kulla a shekarar 2000 zuwa ga ra'ayin Kotun Manyan Laifuka ta Duniya wacce za ta sami ikon magance cin zarafin bil'adama.

Manazarta gyara sashe

  1. "Celebrities 28 04 13". Issuu (in Turanci). Retrieved 2020-05-05.