Yoweri Museveni
Yoweri Museveni ko kuma akirashi da Yoweri Kaguta Museveni, an haifeshi a shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da arba'in da huɗu (1944) a wani wuri da ake cema Mbarra a ƙasar uganda. Ya kasance ɗan siyasa wanda ya zama Shugaban ƙasar a shekara ta 1986. An haifeshi a cikin mutane masu kiwon shanu kuma yaje makarantar masu yaɗa da'awa. Yayi karatun harkar siyasa da tattalin arziki a Jami'an da ake kira da Dar es Salaam a shekara ta 1970 a ƙasar Tanzaniya. Daganan sai ya zama shugaban masu rubutu da hannun hagu da kuma ƙungiyan ɗaukaka Afrika. A lokacin da Shugaban ƙasar mai ci watau Idi Amin a shekara ta 1971, Museveni sai ya gudu ya koma ƙasar Tanzaniya inda ya haɗu da wanda suka taimakamai yaza Shugaban ƙasar ya hanɓarar da Shugaba mai ci shekara ta 1979. Museveni yayi riƙe matsayi acikin gwamnatin riƙon gwarya daganan sai ya tsaya takara a shekara ta 1980 wanda ake tunanin anyi maguɗi wanda ake ganin wanda yaci shine Milton Obote, Museveni da tsohon Shugaban ƙasar Yusufu Lule suka haɗa ƙungiyoyi masu suna Tafiyar masu Jayyaya a turance kuma National Resistance Movement (NRM), Museveni ya Shugabanci ƙungiyan da kuma takwaranta ƙungiyan mai suna Sojojin Masu Jayyaya wanda a turance kuma ake kira da NRM’s armed group, wannan ƙungiyoyin suka watsar da mulkin Obote. Ƙungiyan tayi nasara wanda a watan Junairu 26,alif na 1986 Museveni ya sanar dacewa ya zama Shugaban ƙasar uganda. An kuma zaɓeshi a watan Mayu 9, alif na 1996 wanda kuma suke bayansa suka ci mafi yawan kujeru na majalisan dokokin na ƙasar wanda akayi a watan. Museveni ya sake cin zaɓe a 2001 da kuma 2006 bayan gyara da akayima dokar ƙasar na tsayawa takara. An kuma sake zaɓenshi a shekara ta 2011 and 2016, duk dayake masu sa ido akan harkar tsabe sunce akwai kurakurai da dama a yanayi gudanar da tsaɓen. An sake yima dokar ƙasar garen bawul a 2017 wanda suka cire ƙa'idan shekaru 75 kuma suka maida takara ya zama sau biyu zai iya tsayawa. Ya taimaki ƙasar wurin tattalin arziki, gyara siyasar, da kuma abubuwan morewa na rayuwa. Ya kuma taimaka sosai wurin yaƙi da yaɗuwar cutar ƙanjamau wanda ƙasar na cikin masu yawan cutar a Afrika. Rashawa na daga cikin gwammati Museveni a lokacin da yake mulki, a tsare tsaren ƙasar waje yana taimakawa 'yan adawa sosai a yankin Afrika kamar Laurent Kabila, Sese Seko, Tutsi da daisauransu.[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Amy, Mckenna (21 June,2022). "World leaders". Britannica. Open Publishing. Cite has empty unknown parameter:
|1=
(help); Check date values in:|date=
(help)