Lawan Ahmad
Lawan Ahmad ya kasance dan wasan fim din Najeriya ne,[1] jarumi ne kuma mai shirya fina-finan daracta kuma producer[2] a masana'antar shirya fina-finan Kannywood. Ya fito ne daga "FKD FILM PRODUCTION", ya shigo cikin harkar fim ta hanyar gudummawar Ahmad Suhu. [3]
Lawan Ahmad | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Bakori, 1982 (42/43 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Yusuf Maitama Sule Un AUWALI SANI BENA (en) |
Harsuna |
Turanci Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo |
Tarihin rayuwa
gyara sasheAn haifi Lawan Yahaya Ahmad a Bakori (LGA) da ke a jihar Katsina a ranar 13 ga watan Maris shekara ta alif dari tara da tamanin da biyu 1982. Ya halarci makarantar firamarensa a "Nadabo Primary School Bakori" daga shekara ta alif dari tara da tamanin da bakwai 1987 zuwa shekara ta alif dari tara da casa'in da uku 1993. Ya gama karamar sakandirensa a "Government Day Secondary School Bakori, kuma a karshe ya kammala Babbar Sakandare (SSCE) a "Government Day Secondary School Sharada"daga shekara ta 1994 zuwa shekara ta 2000.
Ya cigaba da karatunsa a "Federal College Of Education Kano daga shekara ta 2002 zuwa shekara ta 2004. Lawan Ahmad ya halarci jami'ar " Yusif Maitama Sule University Kano " daga shekara ta 2016 zuwa shekara ta 2017.
Jarumin ya shiga masana'antar fina -finai ta Kannywood a cikin shekara ta 1999 kuma ya fara fitowa a fim din [SIRADI] wanda ya zama fim dinsa na farko.
Filmography da aka zaɓa
gyara sashe- Zuma
- Sharhi
- Bakace
- Kolo
- Taraliya
- Sansani
- Sai wata rana
- Wasila 2010
- Haske
- Kalamu wahid
- Siradi
- Maya
- Muradin Kaina
- Ni da kai da shi
- Shanya
- Bani ba ke
- Abun da kayi
- Hauwa kulu
Lambobin yabo
gyara sashe- Mafi Kyawun Sabon Comer a fim "ZUMA" daga MTN Awards a 2004
- Fitaccen dan wasa mai tallafi a cikin fim "DA'IMAN" na MTN Awards a shekarar 2016
- Fitaccen jarumin da ya shahara da "Kyautar gwarzon Katsina a shekarar 2017
- Mafi kyawun Jarumi a fim DA'IMAN ta "City People Awards" a cikin 2018
- Fitaccen dan wasa da "AFRO HOLLYWOOD AWARDS LONDON " a cikin Fim "ZAN RAYU DAKE" a cikin 2019
- Mafi Kyawun 'Yan wasa a cikin fim din "Zan Rayu Dake" na Amma Awards Season 5 in 2019.
- Mafi kyawu da birgewa a cikin fim (series film) din "IZZAR SO" tun daga 2020 har zuwa yanzu.
Nasara
gyara sasheLawan Ahmad shi ne Shugaba / GASKIYA na "BAKORI ENTERTAINMENT " dandamalin da ke kwarewa wajen yin fim, samar da abubuwan da ke ciki, da kuma kafofin watsa labarai. Ya shirya fina-finan Haus<<a da yawa kamar: [Ana bukatan hujja][4]
- Shanya
- Bani Bake
- Kolo
- Sadaukarwa
- Abun da ka yi
- Dashen haka
- Koni ko ke
- Izzar so (Series Film)
Manazarta
gyara sashe- ↑ Onuzulike, Uchenna, 1971- (2008). Nollywood video film : Nigerian movies as indigenous voice. VDM Verlap Dr. Müller. ISBN 978-3-639-13564-0. OCLC 678098062.CS1 maint: multiple names: authors list (link)
- ↑ Victoria, Bamas (2018-10-26). "Kannywood's Lawan Ahmed marks 10th wedding anniversary". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2020-09-20.
- ↑ "INTERVIEW: Why I'm the best Kannywood actor – Lawal Ahmad | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2016-04-02. Retrieved 2020-09-20.
- ↑ www.bbc hausa.org.com
Hanyoyin hadin waje
gyara sasheTarihin rayuwa
gyara sasheAn haifi Lawan Yahaya Ahmad an haife shi a yankin karamar hukuma na jihar Katsina a ranar 13 ga watan Maris shekarata alif 1982. Ya halarci makarantar firamare a makarantar firamaren Nadabo Bakori, daga shekarar alif 1987 zuwa shekarata alif 1993. Ya cigaba da Makarantar Sakandare ta gwamnati jika ka dawo, Bakori, don karatun sakandare na ƙarami, kuma ya sami Babban Takardar shaidar Sakandare (SSCE) a Makarantar Sakandaren Gwamnati, Sharada, daga shekara ta alif 1994 zuwa shekarar 2000.
Ya cigaba da karatun sakandare a Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Kano, daga shekarar 2002 zuwa shekara ta 2004. Ya kuma halarci Jami'ar Yusif Maitama Sule ta Kano, daga shekarar 2016 zuwa shekarata 2017.
ɗan wasan kwaikwayo ya shiga cikin masana'antar fina-finai ta Kannywood a cikin shekara (1999) kuma ya fara bayyana a fim din [SIRADI] wanda ya zama fim dinsa na farko.