Cif Lamidi Ariyibi Akanji Adedibu, (An haife shi a ranar 24 ga watan Oktoban a shekara ta 1927 - 11 Yuni 2008) ya kasance dillalin iko a jihar Oyo, Najeriya. Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana shi a matsayin "uba ga jam'iyan PDP".

Lamidi Adedibu
Rayuwa
Haihuwa 24 Oktoba 1927
ƙasa Najeriya
Mutuwa 11 ga Yuni, 2008
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Tarihin rayuwa

gyara sashe

An haife cif Adedibu a ranar 24 ga watan octuba a shekara ta 1927 a garin Oja-Oba, Ibadan, kuma shi daya ne a masarautar Olupoyi .

Adedibu ya Shiga siyasa a shekara ta 1950s, a lokacin shi manba ne na jam'iyan People's Part (PDP), sai kuma daga bisani ya canza zuwa jam'iyar Action Group a karka shin Cif Obafemi Awolowo. Daga bisani ya canza zuwa jam'iyar National Party of Nigeria (NPN) Wanda cif Adisa Akinloye da Richard Akinjide. suke Shugaban ta, a lokacin ganaral Ibrahim Babangida ya Kazan ce a gaba-gaba cikin harkokin siyasa, wanda kuma ya kasan ce yana goyon manjo janar Shehu Musa Yar'adua a jam'iyar Social Democratic Party tare da wasu yan siyasa kamar su Babagana Kingibe, Atiku Abubakar da Abdullahi Aliyu Sumaila.

Siyasan shi siyasa ce da yake amfani da tashin hankali.

An ce babu wanda ya hau wani mukami na siyasa a jihar Oyo ba tare da amincewar Adedibu ba, wanda ya sa aka kira shi "mutum mafi karfi na siyasar Ibadan". An zaɓi dansa, Kamorudeen Adekunle Adedibu, a matsayin Sanatan garin Oyo ta Kudu a watan Afrilun shekara ta 2007. Sanata Teslim Folarin, wanda aka zaba a majalisar dattijai mai wakiltar Oyo ta tsakiya shi ne mai taimaka masa. Rasheed Ladoja, wanda ya zama gwamnan jihar a watan Mayu

Shekara ta 2003, shi ma wani wakilin ne, duk da cewa a watan Agustan shekarar 2004, Ladoja da Adedibu sun kasance cikin mummunan gwagwarmaya kan rabon mukamai.

Adedibu ya rassu a Asibitin koyarwa na Jami'ar Ibadan a ranar 11 ga watan Yuni a shekara ta 2008, ya bar babban mukami da lakabin Ekarun na garin Ibgadan wanda ɗayan da ke ƙarƙashinsa za su maye gurbinsa .

Manazarta

gyara sashe