Abba Kabir Yusuf

Ɗan siyasar Najeriya kuma zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano

Abba Kabir Yusuf Wanda aka fi sani da (Abba gida-gida) ɗan siyasa ne, kuma gwamnan Jihar kano karkashin jam'iyar New Nigeria People's Party (NNPP).wanda ke gudanar da mulki a wannn lokacin

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf
gwamnan jihar Kano

Rayuwa
Haihuwa Gaya, 5 ga Janairu, 1963 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Abba gida gida

[1][2]

Haihuwa da Nasaba

gyara sashe

An haife shi a Jihar Kano, Abba dan Muhammadu Kabir dan dan makwayon Kano Yusuf dan Muhammad Bashir dan Galadiman Kano Yusuf ɗan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo dan kabilar Sullubawa

Karatun sa

gyara sashe
 
Abba Kabir Yusuf

Abba Kabir yayi karatun Primary a Makarantar Sumaila Primary School, ya kammala a Shekara ta 1969-1975. sannan kuma Yayi karatun Sakandire a makarantar Lautai Secondary School Gumel GCE 0/level- a shekara ta 1975-1980. bayan nan ya halarci Federal Polytechnic Yola Jihar Adamawa inda ya sami National diploma ta ƙasa a ɓangaren kimiya da fasaha a fanin injiniya wato(Engineering) A shekara ta 1982-1985, a Kaduna Polytechnic, yayi HND a fannin injiniya a shekara ta 1987-1989 sai kuma ya halarci Jami'ar BUK Kano, PGDM a shekara ta 1994-1995. har wayau ya samu shaidar Masters a bangaren karatun harkokin kasuwanci (MBA) a shekara ta 1997-1999 a Bayero University Kano.

 
Abba Kabir Yusuf

Ya riƙe muƙamin Kwamishinan aiyuka a zamanin mulkin tsohon gwamnan jahar kano Engr.Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, daga shekara ta 2011 Zuwa shekara ta 2015 sannan yayi takarar gwamnan kano a karkashin jam'iyyar PDP a shekara ta 2019.[3] Sannan Kuma ya sake yin takarar Gwamna a jam'iyyar NNPP a jihar Kano a shekara ta 2023.[4] Abba yayi nasarar zama Gwamnan jihar Kano a zaɓen gwamnan Kano na shekara ta 2023 inda kuma yayi nasara a kan babban abokin hamayyar sa na Jam'iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna. An rantsar da Abba kabir yusif a matsayin gomnan jihar kano a ranar Litinin ashirin da tara 29 ga watan Mayu na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023.

Manazarta

gyara sashe