Aminu Ado Bayero An haife shi ne a shekera ta alif dari tara da sittin da ɗaya (1961), shi ne Sarkin Kano na (15), daga ƙabilan Fulani na Sullubawa.[1] Ya hau kan karagar mulki ne a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020, bayan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya sauke sarki Muhammad Sanusi II daga kan karagar mulkin sarautar Kano.[2] shine Chancellor na jami'ar calabar

Aminu Ado Bayero
Rayuwa
Haihuwa Kano, 1961 (62/63 shekaru)
ƙasa Kano
Ƴan uwa
Mahaifi Ado Bayero
Ahali Nasiru Ado Bayero
Karatu
Makaranta Government College, Birnin Kudu
Jami'ar Bayero
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a Emir (en) Fassara

Farkon rayuwa da ilimi gyara sashe

 
Aminu Ado Bayero

Aminu Ado Bayero ya fito ne daga jihar Kano, kuma shi ne na biyu a cikin 'ya'yan Ado Bayero, wato Sarkin kano na (13). Aminu Ado ya halarci makarantar firamare ta ƙofar Kudu sannan ya wuce zuwa makarantar sakandare ta Gwamnati, Birnin Kudu. Aminu Ado ya karanci fannin sadarwa mai yawa daga Jami’ar Bayero Kano, sannan kuma ya tafi Kwalejin Flying, dake Oakland, California, a Amurka,[3] kafin yaci gaba da shiga Ofishin Kula da Matasa na Kasa a Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya, Makurdi.[4]

Kulawa gyara sashe

Aminu Ado ya yi aiki a matsayin jami’in hulda da jama’a a kamfanin jirgin Kabo, kafin ya zama injiniyan jirgin sama. A shekara ta (1990), mahaifinsa, Ado Bayero ya naɗa shi Ɗan Majen Kano kuma shugaban gundumar Dala tun kafin ya kara daukaka shi ga Ɗan Buram ɗin Kano a watan Oktoba na wannan shekarar.[5] A shekara ta (1992) , an inganta shi zuwa Turakin Kano da kuma Sarkin Dawakin Tsakar Gida Kano a shekara ta (2000). Ya kuma yi aiki a matsayin shugaban kwamatin masarautar Kano.[6] A shekara ta ( 2014) , mai martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya daukaka shi zuwa Wamban Kano, don haka ya canza shi daga Dala zuwa karamar hukumar Birni da kewaye, inda ya maye gurbin Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim a matsayin shugaban gundumar.[7]

A shekara ta (2019), gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya naɗa shi a matsayin Sarkin Bichi.[8]

Sarkin Kano gyara sashe

 
Aminu Ado tare da Mayan baki

A ranar (9), ga watan Maris shekara ta (2020), an nada shi a matsayin sarki na (15), na jihar Kano, don maye gurbin Muhammad Sanusi II, wanda aka hambarar dashi a wannan ranar.

Manazarta gyara sashe

  1. ^ Benson, Nneoma (9 March 2020). "Ganduje appoints Aminu Ado Bayero as 15th Fulani Emir of Kano" . The ICIR. Archived from the original on 10 March 2020. Retrieved 9 March 2020.
  2. ^ "Local power play ends the reign of northern Nigeria's emir of Kano · Global Voices" . Global Voices. 19 March 2020. Archived from the original on 9 April 2020. Retrieved 24 April 2020.
  3. ^ ab Mohammed, Farouk (9 March 2020). "Biography of Aminu Ado Bayero, the new Emir of Kano" . okay.ng . Archived from the original on 5 December 2020. Retrieved 9 March 2020.
  4. ^ Adewale, Murtala (18 May 2019). " 'The split of Kano Emirate was never my wish, but things change with time' " . The Guardian Newspaper . Archived from the original on 26 November 2020. Retrieved 9 March 2020.
  5. ^ Alao, Abiodun (9 March 2020). "Five things to know about the new Emir of Kano, Aminu Ado Bayero" . The Nation Newspaper . Archived from the original on 10 March 2020. Retrieved 9 March 2020.
  6. ^ Odeyemi, Joshua (9 March 2020). "Who is Alhaji Aminu Ado Bayero, the new Emir of Kano?" . Daily Trust Newspaper . Archived from the original on 10 March 2020. Retrieved 9 March 2020.
  7. ^ Adewale, Murtala (9 March 2020). "Aminu Ado Bayero may succeed Sanusi as emir of Kano" . The Guardian Newspaper . Archived from the original on 10 March 2020. Retrieved 9 Ma
  8. "Unstoppable Ganduje presents letters to Emir Ado Bayero, 3 others" . P.M. News . 11 May 2019. Archived from the original on 11 May 2019. Retrieved 9 March 2020.