Kabiru Ibrahim Gaya (an haife shi 16 ga Yuni 1952) ɗan siyasa Najeriya ne kuma masanin gine-gine wanda aka zaba a majalisar dattijan Najeriya a shekarar 2007, wanda ya wakilci mazaɓar Kano ta Kudu a jihar Kano a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressive Congress (APC). An zaɓi Kabiru Gaya mataimakin shugaban kungiyar 'yan majalisar tarayya (IPU) na Afirka a babban taron ƙungiyar karo na 135 a Geneva, Switzerland a Oktoba 2016.[1]

Simpleicons Interface user-outline.svg Kabiru Ibrahim Gaya
member of the Senate of Nigeria Translate


gwamnan jihar Kano

Rayuwa
Haihuwa 16 ga Yuni, 1952 (67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Nigeria Peoples Party Translate

Ya halarci makarantar firamare ta Gaya daga shekarar 1961-1964 da Tsangaya Primary School inda ya gama makarantar firamari a shekarar 1968 babban dan uwansa a lokacin shi ne Shugaban Makarantar sannan kuma Abdullahi Aliyu Sumaila shi ne Mataimakin Shugaban makarantar wanda ya koyar da shi Lissafi a makarantar firamare. Ya halarci Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Birnin Kudu daga shekarar 1969 zuwa 1973 inda ya samu takardar shaidar Makarantar Afirka ta Yamma (WASC) da Kwalejin Ilimin Kimiyya daga 1974-1975 inda ya sami IJMB. Ya sami digiri a fannin Gine-ginen daga Jami'ar Ahmadu Bello a 1977[2]

An zabi Kabiru Ibrahim Gaya a majalisar dattijan Kano ta Kudu a 2007. An kuma nada shi a kwamitocin kan gas, Gidaje da na kasashen waje, Jihohi & Kananan hukumomi, da Albarkatun Man Fetur da Ayyuka.[3]

ManazartaGyara

  1. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". Nassnig.org. Retrieved 2020-01-07. 
  2. https://allafrica.com/stories/200301130693.html
  3. https://allafrica.com/stories/200905250350.html?page=3