Kanal Muhammadu Abdullahi Wase shi ne gwamnan jahar Kano na goma sha biyu. Shi mutumin Wase ne ta cikin Jahar Filato.

Muhammadu Abdullahi Wase
gwamnan jihar Kano

Disamba 1993 - ga Yuni, 1996
Kabiru Ibrahim Gaya - Dominic Oneya
Rayuwa
Haihuwa Wase, 1948
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa ga Yuni, 1996
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Farkon rayuwa da Karatu gyara sashe

An haife a shekarar 1948 a garin Wase.

Ya fara karatunsa na ƙaramar firamare (junior primary school) a garin Wase, bayan ya kammala kuma aka tura shi garin Pankshin inda ya yi karatunsa na babbar firmare (Senior Primary School) kamar yadda ake yi da. Daga nan kuma ya samu nasarar shiga Kwalejin Horas da Malamai (Toro Teachers College) da ke Toro. A nan ya fita da sakamakon jarabawa mafi kyau a dukkan faɗin Arewacin Najeriya.[ana buƙatar hujja]

Bayan nan ya wuce zuwa Makarantar Tsaro ta Najeriya (Nigerian Defence Academy (NDA)) da ke Kaduna, a wannan makaranta ma shi ne ɗalibin da ya fi kowa ƙwazo a fannin kadet (Cadet).[ana buƙatar hujja] Ya kammala karatunsa a wannan makaranta ta (NDA) a shekarar 1970. Kanal Muhammadu Abdullahi Wase ya samu nasarar fita ƙasashen waje dan yin kwasawasai. Daga cikin ƙasashen da ya je akwai Ghana, da kuma Birtaniya. Haka nan ma a Najeriya ya halarci kwas a makarantar sojoji ta Jaji. Daga nan kuma ya samu zuwa jami’ar Pittsburgh, inda ya je ya samu digiri na biyu a fannin Mulki. A wannan makaranta ma sai da ya karɓi kyaututtukan da suka haɗa da kyautar ‘Donald Stone Award’[ana buƙatar hujja] da kuma ƙungiyar tsofaffin ɗaliban jami’ar ita ma ta karrama shi.[ana buƙatar hujja] A dai wannan jami’a ta Pittsburgh ya sake canja fanni ya koma fannin injiniyarin ya sake yin digiri na biyu (M.Sc Transport Engineering and Management).

Aiki da Siyasa gyara sashe

Tun gama digirinsa na farko a makarantar soja (NDA) ta Kaduna, makarantar ta riƙe shi ta bashi aikin kwamanda (Officer Commanding Demonstration Company). Sannan kuma ya riƙe muƙamin darakta har zuwa shugaban hukumar zaɓen Nijeriya lokacin tana (NEC) wato (National Electoral Commision).

Gwamnan Kano gyara sashe

Kanal Wase ya zamo gwamnan jahar Kano a shekara ta 1993, Muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 1996.

Ayyuka gyara sashe

Kanal Muhammadu Abdullahi Wase ya bayar da gudunmawa mai gwaɓi wajen ci gabanjahar Kano da haɓɓaka tattalin arziƙin jahar. Kusan babu wani ɓangare na jahar Kano da Kanal Wase bai taɓa ba. Imma dai kai tsaye ko kuma a fakaice, kamawa tun daga ɓangaren mulki, zuwa kasuwanci, lafiya, sufuri, walwala da jin daɗin jama’a, fannin noma, fannin ilimi da sauransu. [1]

Tituna Ya faɗaɗa gidan gwamnatin jahar Kano, ya gina tituna arba’in a karkara, shi ya gina titin eastern by-pass, ya kawo motocin sufuri guda goma masu kujeru 39 sannan kuma ya bada kuɗin da yawansu ya kai Naira Miliyan 41.4 dan gina gurin gyara da sayo safaya fat. [2]

Dala building Society Shi ya kafa bankin Dala (Dala Building Society), ya ƙarasa ginin masallaci da asibiti da ke sakatariyar Audu Baƙo, ya gina Wuman santa (Women Centre) da ke kan titin Zariya, ya gina magudanan ruwan da tsayinsu ya kai mita 575 da kuma wasu da tsayinsu ya kai mita 3000.

Manazarta gyara sashe